An kashe mutum daya tare da raunata akalla mutum 200 a fadin kasar Kenya a ranar Alhamis a zanga-zangar adawa da shirin gwamnati na tara dala biliyan 2.7 a karin haraji, in ji ƙawancen kungiyoyin kare hakkin bil adama da kuma hukumar 'yan sanda.
'Yan sanda sun harba hayaƙi mai sa hawaye da fesa ruwan zafi domin tarwatsa masu zanga-zanga a Nairobi babban birnin kasar, kamar yadda kungiyoyin kare hakkin ɗan'adam biyar da suka hada da Amnesty International da kungiyar likitocin Kenya suka faɗa a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a yammacin jiya Alhamis.
Sun ce harsasan da aka gani a ƙasa burjik sun nuna cewa na gaske ne aka yi amfani da su wajen harbe-harbe, inda suka ƙara da cewa an kama masu zanga-zanga sama da 100 a fadin Kenyan.
Hukumar sa ido kan ‘yan sanda mai zaman kanta (IPOA) ta ce a ranar Juma’a ta tattara bayanan mutuwar wani mutum “sakamakon harbin da ‘yan sanda suka yi da wasu munanan raunuka da wasu masu zanga-zangar ciki har da ‘yan sanda suka ji.
Kira don a yi watsi da ƙudurin dokar kudi
Mutumin mai shekara 29 ya mutu ne a lokacin da ake duba masa raunin da ya samu a cinyarsa a wani asibiti a ranar Alhamis da daddare, kamar yadda rahoton 'yan sanda ya gani, wanda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito. Rahoton bai bayyana yadda ya jikkata ba.
Kwamandan 'yan sandan gundumar Nairobi Adamson Bungei bai amsa kiran waya don jin ta bakinsa ba.
"Muna yaba wa dubban masu zanga-zangar, wadanda yawancinsu matasa ne, saboda sun yi ta cikin lumana (da kuma) nuna kamun kai duk da tsokanarsu da 'yan sanda suka yi," in ji kungiyoyin kare hakkin ɗan'adam ɗin.
Masu zanga-zangar dai na son gwamnati ta yi watsi da kudirin nata na kudi gaba daya, suna masu cewa hakan zai dagula tattalin arzikin kasar tare da ƙara tsadar rayuwa ga ‘yan kasar Kenya wadanda tuni ke fafutukar ganin sun biya bukatunsu.
Shugaban Ƙasa ya sassauta ƙudurin
Asusun ba da lamuni na duniya IMF, ya ce akwai bukatar gwamnati ta kara yawan kudaden shiga domin rage gibin kasafin kudi da rancen jihohi.
A farkon makon nan ne gwamnatin kasar ta dan sassauta matsayarta, inda shugaban kasar William Ruto ya amince da soke wasu sabbin harajan da suka hada da na mallakar motoci da na biredi da man girki da hada-hadar kudi.
Duk da zanga-zangar da ta barke a gundumomi 19 daga cikin 47 na kasar Kenya, ‘yan majalisar sun amince da kudirin dokar kudi a karatu na biyu a ranar Alhamis, inda suka matsar da shawarwarin harajin da ake takaddama a kai zuwa mataki na gaba domin amincewa.
A ranar Talata ne ake sa ran ‘yan majalisar za su yi taro domin kada kuri’a kan sauye-sauyen da ake shirin yi wa kudirin, wanda kwamitin kasafin kudi na majalisar ya ce zai kashe zunzurutun kudi har biliyan 200 na Kenya (dala biliyan 1.56) a cikin kasafin kudin shekarar 2024/2025, tare da tilasta wa gwamnati ta rage kashe kudade.