Ana fargabar samun yunwa a Sudan saboda kawo cikar ga ayyukan raba kayan abinci. / Hoto: AFP Archive

Ƙazamin rikici ya ɓarke a ranar Lahadi tsakanin sojojin Sudan da mambobin rundunar ɗaukin gaggawa ta RSF a jihohin Khartoum, Al Jazirah da White Nile, da kuma garin El Fasher, kamar yadda ganau suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

Sun bayyana cewar sojoji sun kai farmaki ta sama kan cibiyoyin da dakarun RSF suke taruwa a kusa da matatar man fetur ta Jaili, arewa da babban birnin Khartoum, suna mai ƙarawa da cewar an ga hayaƙi ya turnike sararin samaniya a yayin da aka kai hare-haren ta sama.

Har yanzu RSF na riƙe da ikon yankuna da dama a garin Bahri da ke arewa da Khartoum, ciki har da matatar mai ta Jaili, inda sojojn ƙasar kuma ke jibge a unguwanni da dama na garin da ma'ajiyar makamai ta Hattab da Kadroo.

Jiragen yaƙin rundunar sojin sun kai farmakai kan yankunan kudancin Khartoum da gundumar Alkotainh a jihar White Nile, kamar yadda ganau suka tabbatar.

Kwamitin Tirjiya na Wad Madani ya bayyana cewa wani jirgin saman soji ya kai farmaki kan RSF a ƙauyen Bika, yamma da garin Wad Madani, babban birnin jihar Al Jazirah.

Fagen gumurzu: El Fasher

Tun watan Disamban shekarar da ta gabata, RSF ke riƙe da iko da garuruwa da dama a jihar Jazirah ciki har da Wad Madani. Ganau sun ce arangama ta sake ɓarkewa tsakanin sojoji da dakarun RSF a arewaci da gabashin El Fasher, inda aka yi amfani da manyan makamai.

Sun ƙara da cewa sojojin sun ƙaddamar da farmakai ta sama kan dandazon dakarun RSF a gabashin El fasher.

A ranar Lahadin da ta gabata, hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanar da ɓarkewar arangama a ranar Asabar tsakanin sojoji da dakarun RSF a unguwannin yammaci da kudu maso-gabashin El Fasher, wadda ta janyo tsugunar da iyalai 250 da kuma samun jikkata ko rasa rayuka.

Sojojin Sudan ko dakarun RSF babu wanda ya ce wani abu game da wannan al'amari.

Yaƙin Sudan

Tun 10 ga Mayu ake aranama tsakanin sojoji da dakarun a El fasher duk da cewa a baya sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, yayin da ƙasashen duniya suka yi gargaɗi kan rikici a garin wanda ya kasance cibiyar jigilar kayan agaji ga yankin Darfur.

Ana ta samun ƙarin kiraye-kiraye daga Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa don kawar da bala'in jinƙai da zai jefa miliyoyin mutane cikin hatsarin yunwa da mutuwa saboda ƙarancin kayan abinci da rikicin ya janyo a jihohi 12 daga cikin 18 na ƙasar.

Kira na baya-bayan nan ya fito daga Asusun Tallafawa Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) inda suke neman a tsagaita wuta nan-take a Sudan "don kawar da yunwa da ke yin barazana da kuma nisantar kashe yara ƙanana."

Tun tsakiyar watan Afrilun bara, sojojin Sudan da dakarun RSF suka fara yaƙi, wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka kusan 15,000 da tsugunar da sama da mutane miliyan takwas, kamar yadda MDD ta bayyana.

TRT World