Kasar Burkina Faso ta ƙaddamar da sabbin fasfo din tafiye-tafiye wanda ba ya ɗauke da tambarin babbar Ƙungiyar Raya Tattalin Arziki Ƙasashen Yammacin Afirka, lamarin da ke ƙara nuna aniyarta ta ficewa daga ƙawancen yankin bayan da shugabannin sojoji suka karbe mulki a wani juyin mulki.
Kasashen Burkina Faso da Nijar da kuma Mali da ke karkashin mulkin soja a yanzu sun sanar da cewa a cikin watan Janairu tare da hadin gwiwarsu za su fice daga kungiyar ECOWAS mai mambobi 15, wadda tun daga lokacin ƙungiyar take kokarin shawo kansu da su sake yin la'akari da matakin da suka dauka.
"A kan wannan fasfo ɗin babu tambarin ECOWAS, kuma babu inda aka rubuta ECOWAS a jiki. Tun watan Janairu, Burkina Faso ta yanke shawarar janyewa daga ƙungiyar, kuma wannan matakin alama ce da ke nuna bin hukuncin da Burkina Faso ta yanke," kamar yadda Ministan Tsaro Mahamadou Sana ya shaida wa manema labarai a ranar Talata.
Magance rashin tsaro
Tuni ECOWAS ta gargaɗi ƙasashen uku kan cewa janyewar tasu za ta shafi fafutukar 'yanci da kasuwar bai-ɗaya ta mutum miliyan 400 da ke zaune a ƙasashen ƙungiyar mai shekara 50.
Ficewarsu ta zo ne a lokacin da dakarunsu ke yaƙi da ƙungiyoyi masu alaƙa da al Qaeda da Daesh, waɗanda ta'addancinsu ke taɓarɓarar da zaman lafiya a Yammacin Afirka a tsakiyar yankin Sahel fiye da shekara 10 tare da barazanar bazuwa a ƙasashen da ke kusa da gaɓar teku.
Tun bayan da sojojinsu suka ƙwace mulki cikin jerin juyin mulki tsakanin shekarar 2020 zuwa 2023, kasashen uku sun kulla yarjejeniyar tsaro da hadin gwiwa ta hanyoyi uku da aka fi sani da kawancen kasashen Sahel tare da yanke huldar soji da diflomasiyya da ta dade da Ƙasashen Yammacin Duniya, tare da neman sabbin abokan hulɗa a kasashen waje.