Gwamnatin ta Kano ta yi kira ga jami'an tsaro su janye jami'an da suka rufe hanyoyin shiga wajen taron, tana mai cewa za a gudanar da taron kamar yadda aka shirya. / Hoto: Instagram/Abba Kabir

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gargaɗi jama’ar Birnin jihar kan yiwuwar kai harin ta’addanci a birnin a cikin kwanankin nan, tana gargaɗin jama’a su kaurace wa wuraren taruwar jama’a.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Juma’a ta ce rundunar “ta samu bayanan sirri kan wasu da suke shirin kai wa jama’a harin ta’addanci a wasu muhimman wurare a Jihar Kano.”

“Don haka muna kira ga jama’a su yi taka-tsantsan kuma su ƙaurace wa wuraren taruwar jama’a har sai nan da wani lokaci, a matsayin wata hanyar kariya, don bai wa jami’an tsaro damar ganowa da kuma daƙile yiwuwar kai harin,” a cewar sanarwar ta Kiyawa.

Kakakin ‘yan sandan ya ce, jami’an tsaro sun ɗauki matakin daƙile duk wata barazana.

Ya ce tuni akan tura ƙwararru daga ɓangarorin rundunar masu kwance bam, da masu kula da sinadarai masu guba, da masu kula da ɓangaren makamin nukiliya zuwa wasu muhimman wurare, kuma suna cikin shirin ko-ta-kwana.

‘Babu wata barazanar tsaro’

Sanarwar da Kiyawa ya sanya wa hannu ta kuma bayar da lambobin waya, domin kai rahoton duk wani abu da jama’a suka gani da ba su amince da shi ba.

Sanarwar da rundunar ‘yan sanda ta Kano ta fitar ta zo ne kwana ɗaya gabanin taron maulidin Sheikh Ibrahim Inyass da ɓangaren Khalifan Tijjaniyya Sarki Muhammadu Sanusi II ya shirya gudanarwa a birnin a ranar Asabar ɗin nan.

Tuni dai jami’an tsaro suka toshe duk wasu hanyoyi da za a bi a je wajen da aka shirya gudanar da taron.

To sai dai gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da sanarwar ta ‘yan sanda, ta yi Allah-wadai da ita, inda ta bayyana ta a matsayin mara tushe balle makama.

Gwamnatin ta kuma yi kira ga jami’an tsaro su janye jami’an da suka killace wajen da za a gudanar da taron na maulidin da ‘yan Tijjaniyya suka shirya.

A yayin wani taron manema labarai a ranar Juma’a, Kwamishinan Watsa Labarai da Al’amuran Cikin Gida na Kano, Kwamared Ibrahim Wayya ya ce, an fitar da gargaɗin ne don hana taron maulidin na ƙasa da aka shirya gudanarwa a Kano.

Kwamishinan ya ce babu dalilin ɗaukar wannan mataki domin “babu rahoton wata barazanar tsaro a duka faɗin jihar da za ta sa a ɗauki irin wannan tsattsauran mataki,” yana mai nuna shakku kan inda jami’an tsaro suka samu bayanin.

Tuni dai baƙi daga ciki daga wajen Nijeriya suka fara shiga birnin don gudanar da maulidin a filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata a tsakiyar birnin.

Haka kuma wani ɓangaren na mabiya Tijjaniyya ƙarƙashin Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya shirya gudanar da wani maulidin na Sheikh Ibrahim Inyass a garin Bauchi a ranar Asabar ɗin.

TRT Afrika da abokan hulda