Rundunar Sojin Sudan ta ce ta tarwatsa ƙawanyar da dakarun Rapid Support Forces (RSF) suka yi wa hedikwatarta da ke birnin Khartoum, wadanda suka kewaye hedikwatar tun bayan ɓarkewar yaki a watan Afrilun 2023.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma'a, rundunar ta ce sojojin da ke Bahri (Khartoum ta Arewa) da Omdurman da ke gabar Kogin Nilu sun "hade da sojojinmu da ke a babbar hedikwatar rundunar ta soji".
Wata majiyar soji ta tabbatar da cewa "shigowar dakaru daga Bahri nan take ya kawo ƙarshen ƙawanyar a hedikwatar.”
Rundunar ta kara da cewa ta kori RSF daga matatar mai ta Jaili da ke arewa da babban birnin kasar, wadda ita ce mafi girma a kasar, wadda rundunar sojojin ta yi ikirarin cewa tana da iko da ita tun farkon yakin.
A cikin wata sanarwa da RSF ta fitar ta yi watsi da ikirarin da sojojin Sudan din suka yi a matsayin farfaganda da aka tsara domin ƙara ƙarfin gwiwa ta kuma zargi sojojin da yada labaran karya ta hanyar haɗa faifan bidiyo na bogi.
Faɗan da aka yi a kusa da matatar man ya ƙona rukunin da ke bazuwa, bayanan tauraron dan adam da kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya yi nazari a kai a ranar Asabar ya nuna hayaƙi mai kauri yana tashi daga sararin samaniya.
Matatar man mallakin gwamnatin Sudan ce da kuma kamfanin mai na kasar China National Petroleum Corp.
Tun bayan barkewar yaƙin da sojojin Sudan a watan Afrilun 2023, RSF yi wa Siginal Corps a Arewacin Khartoum ƙawanya da kuma babbar hedikwatar tsaro.