Janar AE Abubakar ya ce babban burinsu shi ne wanzar da tsaro a fadin Nijeriya,/ Hoto: Rundunar Sojin Nijeriya

Rundunar Sojojin Nijeriya ta kaddamar da wani gagarumin shiri na kwace haramtattun makamai daga wurin bara-gurbi a jihohin Filato da Bauchi da Kaduna.

Kwamandan rundunar Operation Safe Haven Janar AE Abubakar, wanda ya kaddamar da shirin a karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato a ranar Talata, ya kara da cewa babban burinsu shi ne a samu cikakken tsaro a jihohin da ma fadin Nijeriya.

Jihar Filato ta kwashe shekaru aru-aru tana fama da rikicin kabilanci musamman tsakanin 'yan kabilar Birom da kuma Fulani, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane. Su ma jihohin Kaduna da Bauchi na fama da irin wadanda matsaloli, ko da yake a yanzu hare-haren 'yan bindiga masu garkuwa da mutane sun fi damun jihar Kaduna.

Janar Abubakar ya ce "dole ne hukumomi su magance silar rikice-rikicen da ke addabar" jihohin "domin a kawar da rashin tsaron da ke damun al'ummominsu".

Labari mai alaka: Sojojin Nijeriya sun ragargaji 'yan bindiga a Mangu ta Filato

"A yayin da nake mika umarnin Hafsan Hafsoshin Tsaron Nijeriya cewa dole ne a dauki dukkan matakin da ya kamata na hana bazuwar rikici a karamar hukumar Mangu, ina kira a mutunta sarakunan gargajiya a matsayinsu na masu wanzar da zaman lafiya," in ji Janar Abubakar.

Janar Abubakar ya yi kira ga sarakunan gargajiya su ci gaba da taka muhimmiyar rawa don tabbatar da tsaro a Nijeriya./Hoto: Rundunar Sojin Nijeriya

A nasu bangaren, sarakunan gargajiya sun sha alwashin ci gaba da goyon bayan hukumomin tsaron Nijeriya a yunkurinsu na wanzar da zaman lafiya a kasar.

TRT Afrika