Mayaka dauke da makamai sun kai hari wani birni a yankin Darfur inda suka rika gwabza fada a tsakaninsu, suna fasa shaguna da sace-sace a daidai lokacin da janar-janar da ke yaki a Sudan suka amince su tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta ta awa 72 da suka kulla.
Yamutsi ya faru ranar Alhamis a birnin Genena na Darfur yayin da rikicin da janar-janar din suke yi a Khartoum, babban birnin Sudan yake watsuwa zuwa wasu yankunan.
Bangarorin biyu sun amince su tsawaita yarjejeniyar ce ranar Alhamis da daddare.
An cigaba da fafatawa tsakanin dakarun sojin Sudan da ke karkashin Janar Abdel Fattah Al-Burhan da dakarun Rapid Response Force, RSF da ba na gwamnati ba, da ke karkashin Janar Mohamed Dagalo duk da yarjejeniyar tsagaita wutar wadda Amurka da Majalisar Dinkin Duniya suka sa baki.
Yarjejeniyar ta bayar da dama don kwashe daruruwan 'yan kasashen wajen da ke son ficewa daga Sudan.
Darfur ya zama fagen-daga
Ganau sun ce an ci gaba da gwabza fada tsakanin sojin Sudan da dakarun RSF a babban birnin kasar da kuma yankin Darfur wanda ya dade a cikin rikici.
Hasalima yankin na Darfur ya zama wani fagen-daga tsakanin bangarorin biyu tun da rikici ya kaure kusan makon biyu da suka gabata.
Ranar Alhamis, mayakan da ke sanye da kakin rundunar RSF sun kai hari a yankuna da dama na birnin Genena, inda suka kori mutane daga gidajensu.
Rikicin ya watsu ne bayan mayakan da ke ikirarin kare kabilunsu sun shiga cikinsa a Genena, birnin da ke kan iyakar kasar da Chadi.
"Ana kawo hare-hare ne daga kowane bangare," a cewar Amany, wani mazaunin Genena. "Kowa yana guduwa daga nan."