Rikicin Masarautar Kano: An tura ƙarin 'yan sanda Fadar Sarki ta Ƙofar Kudu da Gidan Nasarawa

Rikicin Masarautar Kano: An tura ƙarin 'yan sanda Fadar Sarki ta Ƙofar Kudu da Gidan Nasarawa

Kwamishinan 'yan sandan jihar mai barin gado Usaini Gumel ne ya bayyana haka a hira da manema labarai ranar Litinin a birnin Kano.
A makon jiya ne wata kotun tarayya da ke Kano yanke hukunci da masana ke kallo a matsayin mai rikitarwa kan dambarwar da ake yi tsakanin Muhammadu Sanusi na II da Aminu Ado Bayero kan masarautar Kano.

Rundunar 'yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta ce ta tura ƙarin jami'ai a fadar Sarki na 14 Muhammadu Sanusi na II da ke Ƙofar Kudu da kuma Gidan Nasarawa, inda Sarki na 15 Aminu Ado Bayero yake da zama.

Kwamishinan 'yan sandan jihar mai barin gado Usaini Gumel ne ya bayyana haka a hira da manema labarai ranar Litinin a birnin Kano.

Ya ƙara da cewa sun ɗauki matakin ne "domin daƙile duk wata barazana da ka iya tasowa a waɗannan wurare.”

“An tura ƙarin jami'an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a Fadar Ƙofar Kudu, gidan Sarki Malam Muhammadu Sanusi, da kuma ƙaramar fada ta Nasarawa, inda Sarki Aminu Bayero yake da zama,” in ji shi.

Kwamishina Gumel ya yi kira ga mazauna birnin na Kano su ci gaba da bai wa 'yan sanda haɗin kai ta hanyar ba su duk wani labari da zai tabbatar da tsaron jihar.

TRT Afrika