Daga ranar Litinin 29 ga watan Mayun da aka rantsar da shi, Gwamna Abba ya bayyana daukar jerin matakai ba tare da bata lokaci ba /Hoto: Kano Govt  

Jim kadan bayan shan rantsuwar kama mulki da sabon gwamnan Jihar Kano a arewacin Nijeriya Abba Kabir Yusuf ya yi, ya sanar da fara daukar wasu matakai a jihar.

Gwamnan, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, yana daga cikin sabbin gwamnonin da suke jan hankali ba ma a Kano ba kawai, har a fadin kasar da ma tsakanin ‘yan Nijeriya mazauna wasu kasashen.

Sannan zafin da adawa ta yi tsakanin bangaren Abba Gida-Gida karkashin jagorancin uban gidansa kuma uban jam’iyyarsa ta NNPP, Rabiu Kwankwaso da bangaren gwamnatin da ta sauka ta Abdullahi Ganduje na APC, ta sake zama batun tattaunawa.

Hakan ya sa mutane suke bibiyar duk wani motsi na gwamnan tun daga lokacin yakin neman zabensa har zuwa inda nan ke motsi.

Daga ranar Litinin 29 ga watan Mayun da aka rantsar da shi, Abba ya bayyana jerin wasu matakai da ya dauka ba tare da bata lokaci ba.

Matakai na baya-bayan nan da ya sanar da daukarsu sun hada da bai wa hukumomin tsaro umarnin kwato da wasu filaye da kadarorin da gwamnatin da ta gabata ta sayar da sake bude makarantu 26 na koyar da sana’o’i.

Matakan sun hada da:

Nade-naden mukamai

  • Injiya Abba Kabir ya nada Dokta Abdullahi Baffa Bichi, jigo a NNPP, a matsayin sakataren gwamnatin jihar
  • Shehu Wada Sagagi a matsayin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano
  • Dokta Farouq Kurawa a matsayin - Babban Sakataren da ke yi wa gwamna hidima
  • Honorabul Abdullahi Ibrahim Rogo - Babban mai kula da tsare-tsaren gwamna
  • Sunusi Bature Dawakin-Tofa - Mai magana da yawun gwamna.

Rusa kwamitin gudanarwa na hukumar jin dadin alhazai

Gwamna Abba Kabir ya kuma sanar da rushe kwamitin gudanarwa na hukumar jin dadin alhazai ta Jihar Kano.

Ya nada sababbin shugabannin kwamitin kamar haka:

  • Alhaji Yusuf Lawan - Shugaba
  • Alhaji Laminu Rabi’u – Babban Sakatare
  • Shiek Abbas Abubakar Daneji - Mamba
  • Shiek Shehi Shehi Maihula- Mamba
  • Amb. Munir Lawan- Mamba
  • Shiek Isma'il Mangu, Mamba
  • Hajia Aishatu Munir Matawalle- Mamba
  • Dr. Sani Ashir- Mamba

An umarci sababbin shugabannin da su karbi ragamar ci gaba da gudanar da al’amuran hukumar don ayyukan Hajjin bana su tafi lafiya.

Sake bude cibiyoyin koyar da sana’o’i 26

A wata sanarwa da ya wallafa ranar Talata kuma a shafinsa, sabon gwamnan ya ce ya ba da umarnin sake bude makarantun koyar da sana’o’i 26 da aka kafa tun lokacin mulkin Rabi’u Musa Kwankwaso, amma gwamnatin Abdullahi ganduje ta rufe su.

Ziyara ta farko da Abba ya kai zuwa gidan sauya dabi'u ne na Kiru /Hoto: Kano govt

“Nan ba da dadewa ba za a fara daukar mutane don karatu a makarantun, wadanda tun asali aka kafa su don koya wa mata da matasa sana’o’i,” in ji gwamnan.

Sake bude makarantar gyaran hali

Ziyara ta farko da Abba Gida-Gida ya kai jim kadan bayan rantsar da shi a ranar Litinin ita ce zuwa Makarantar Gyaran Hali ta Kiru da ya ce ita ma kwanan nan za a sake bude ta don sauya dabi'un masu tu’ammali da miyagun kwayoyi.

“Ganin yadda ake samun karuwar fashi da makami musamman na wayoyi da sauran miyagun laifuka da ake aikatawa a titunan jiharmu, mun samar da wata hukuma ta hadin gwiwar jami’an tsaro don yakar wadannan laifuka.

“Hukumar hadin gwiwar ta hada da tawagogin hukumomin tsaro da kotunan tafi da gidanka da za su dinga aiki don tsaftace titunanmu daga miyagu tare da gurfanar da su a gaban kotu cikin gaggawa.”

Kwato filayen gwamnati da aka sayar

Gwamna Abba ya ce duba da shawarar da kwamitin karbar mulkinsa ya bayar, “ina sanar da cewa hukumomin tabbatar da tsaro za su kwace iko da duk wasu wurare mallakar gwamnati da aka sayar ba bisa ka’ida ba karkashin mulkin Ganduje.

“Mun fahimci cewa gwamnatin da ta gabata ta sayar da filaye da ke kewayen makarantu da wuraren ibada da asibitoci da makabartu da wuraren tarihi da ke gefen ganuwar Kano.

“Sannan mun gano cewa sun sayar da kadarori da dama malakar gwamnatin Jihar Kano ga wakilansu da na jikinsu,” a cewar sabon gwamnan.

Bijiro da batun neman Dadiyata

A tun jawabinsa na farko bayan shan rantsuwar mulki, Injiniya Abba Kabir ya ce gwamnatinsa ba za ta manta da batun Abubukar Dadiyata ba, “wani babban magoyin bayanmu da aka sace fiye da shekara uku da suka wuce.”

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta yi maraba da wannan batu. Hoto/Kano gov

Gwamnatin Jihar Kano za ta sake bijiro da zancen nan ta hadin gwiwa da dukkan hukumomin tsaro na kasar don ceto shi da kuma gurfanar da wadanda ke da hannu a batan nasa a gaban kuliya.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta yi maraba da wannan batu.

Kazalika mutane daga fadin kasar sun yi ta jinjina wa matakan da Abba Gida-Gida ya sanar da dauka ta hanyar yin tsokaci a kasan sakonnin da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta.

TRT Afrika