Gwamnatin Ghana ta yi watsi da wani rahoton da ke cewa 'yan bindiga a Burkina Faso na amfani da arewacin Ghana a matsayin wani sansani da ajiye kayan aiki da kuma kiwon lafiya domin ci gaba da tayar da ƙayar baya.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, ma’aikatar tsaro ta Ghana ta ce ba ta da wata yarjejeniya da ke tsakaninta da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.
“Ma’aikatar na Allah wadai da kakkausar murya kan ɗaukar Ghana da ake yi a matsayin ‘hanyar samar da kayayyaki’ ga ‘yan bindiga.
Ƙawayen Ghana na jinjina mata kan aikin da take yi na yaƙi da ta’addanci a yankin da duniya,” in ji sanarwar. Ya kara da cewa jami'an tsaron kasar na taka rawar gani wajen yaki da ta'addanci musamman a kan iyakar arewacin Ghana.
Tsallaka iyakoki
Gwamnatin Ghana ta hanyar hukumominta na tsaro da leken asiri na ci gaba da gudanar da ayyukanta na dakile duk wani kutse na ‘yan ta’adda ko kuma tsallaka iyakoki da ‘yan ta’adda ke yi, kuma tana yin hakan tsawon shekaru tare da samun gagarumar nasara,” in ji sanarwar.
Kasar Ghana dai na da iyaka mai nisan kilomita 600 da Burkina Faso, kasar da ke fama da rikici wanda ke da nasaba da kungiyar Al Qaeda da kuma kungiyar Daesh wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu a yankin Sahel na yammacin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara.
‘Yan ta’adda sun ƙara ƙarfi a sama da shekara 12 da suka gabata duk da kuɗin da ake kashewa ta hanyar gayyato sojojin ƙasashen waje domin yaƙi da su.