A yayin da ake tunawa da ranar jinkai ta duniya, wani babban batu da ya fito fili shi ne irin rawar da kasashe suke takawa wurin bayar da agaji ga mabukata.
Kididdigar Global Humanitarian Overview game da ayyukan jinkai ta nuna cewa Turkiyya ce kasa ta biyu da ta fi bayar da agaji a duniya baya ga Amurka.
Sai dai ita ce kasar da ta fi tausaya wa masu bukatar jinkai idan aka kwatanta da kudin shigarta na shekara.
A jawabin da ya yi ga daliban Jami'ar Hacı Bayram Veli da ke Ankara a watan Oktoba na 2022, shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana irin gudunmawar da kasar take bayarwa a fadin duniya ta hanyar ayyukan agaji.
Alkaluma sun nuna cewa a 2021 ta bayar da agajin fiye da dala biliyan 5,587. A 2020, agajin da kasar ta bayar sun kai dala biliyan 8,036.
Turkiyya ta kusa ninka agajin da take bayarwa tun daga 2014: daga dala biliyan 3.2 billion zuwa dala biliyan 5.587 a 2021, sai kuma adadi mafi yawa da ta bayar na dala biliyan 8.036 a 2020.
Ayyukan jinkai da Turkiyya, wanda kasar ta soma a tsakiyar shekarun 1980 ta hanyar bayar da agajin abincin, sun karu sosai zuwa sassan duniya.
Ankara ta bayar agajin kudi da na kayayyaki ga wuraren da suka gamu da bala'o'i irin su ambaliyar ruwa, fari, gobara, girgizar kasa da mahaukatan guguwa.
A 2019 Turkiyya ta bai wa Mozambique agaji bayan mahaukaciyar guguwar Idai ta auka wa lardin Beira, lamarin da ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane. Kazalika ma'aikatar lafiyar kasar ta bayar da agajin magunguna da sauran kayan kiwon lafiya.
A shekarar ce, Turkiyya ta bayar da agajin gaggawa ga Burkina Faso, Algeria, Djibouti, Chadi, Ethiopia, Gambia, Sudan ta Kudu, Kamaru, Comoros, da Namibia.
Haka kuma ta bayar da irin wannan agaji ga Nijar, Somalia, Sudan, Tanzania, da kuma Tunisia.
Turkiyya tana shan yabo game da irin wadannan tallafi da take bayarwa a yayin da a nata bangaren take ci gaba da bullo da hanyoyin saukaka wa al'ummar duniya radadin da suke fama da shi.