Majalisar dattawan Nijeriya ta amince da bankin raya kasa na China a matsayin wanda zai ba da rancen $973 don gina layin dogo da zai tashi daga jihar Kaduna zuwa Kano.
Hakan na zuwa ne bayan da wani bankin da ke ba da lamuni na kasar China ya janye daga aikin a 2020, kamar yadda ‘yan majalisar suka bayyana a zamansu na ranar Talata.
Ita ma Majalisar wakilan kasar ta amince a bai wa bankin wannan aiki wanda zai ba da lamuni na tsawon shekaru 15 a kan kudin ruwa kashi 2.7 cikin dari.
Majalisar dokokin Nijeriya ta sha amincewa gwamnati ta karbo bashi daga China da wasu kasashen waje don gina layin dogo.
A 2022 ne Nijeriya ta nemi bankin Standard Chartered Bank ya ba ta bashin kudin da za a gina layin dogo daga Kano zuwa Maradi, bayan da ta samu jinkiri daga masu ba ta lamuni na kasar China.
Sai ga shi yanzu gwamnati ta sake komawa China don neman bashin kudi.
Shugaba Buhari na kasar ya sha alwashin inganta harkokin sufuri da samar da wutar lantarki da sauran fannonin jin dadin rayuwa.
A watan Mayun shekarar nan shugaban kasar zai mika mulki ga zababben shugaban Nijeriya Bola Tinubu, wanda ya yi alkawarin magance dimbin matsalolin da suka addabi kasar.