Wannan sabuwar yarjejeniyar ta ƙunshi yadda za a samu ci gaba a aikin na Trans-Saharan Gas Pipeline (TSGP). / Hoto: Reuters

Nijeriya, Nijar da Aljeriya sun saka hannu kan wata yarjejeniya wadda za ta bayar da dama a gaggauta kammala aikin shimfiɗa bututun iskar gas wanda ya taso tun daga Nijeriya ya ratsa ta Nijar zuwa Aljeriya.

Wannan sabuwar yarjejeniyar ta ƙunshi yadda za a samu ci gaba a aikin na Trans-Saharan Gas Pipeline (TSGP).

An saka hannu kan wannan sabuwar yarjejeniyar ne a Algiers babban birnin Aljeriya a lokacin da aka gudanar da taro karo na huɗu na kwamitin gudanarwa na aikin TSGP.

Waɗanda suka saka hannu a yarjejeniyar sun ƙunshi Ƙaramin Ministan Makamashi na Aljeriya Mohamed Arkab da Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur na Nijeriya Ekperikpe Ekpo da Ministan Man Fetur na Nijar Sahabi Oumarou da kuma Ministan Tsafta da Muhallai na Nijar Maizama Abdoulaye.

An ƙirƙiro wannan aikin na shimfiɗa bututun iskar gas wanda zai tashi daga Nijeriya ya ratsa ta Nijar da kuma Aljeriya da zummar fitar da gas ɗin zuwa kasuwannin Turai da sauran ƙasashen duniya.

Sai dai saka hannu kan yarjejeniyar na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar matsalar tsaro a yankin na Sahel, wanda ake ganin yana cikin abubuwan da ya rinƙa kawo cikas a tafiyar da aikn

TRT Afrika da abokan hulda