Mataimakiyar shugaban ƙasar Namibia kuma 'yar takarar jam'iyya mai mulki Netumbo Nandi-Ndaitwah ta zama mace ta farko da ta lashe zaɓen shugaban ƙasar wanda aka gudanar a makon jiya.
Alƙaluman da hukumar zaɓen ƙasar ta fitar sun nuna cewa Nandi-Ndaitwah, mai shekara 72, ta jam'iyyar South West Africa People's Organization (SWAPO) ta samu kashi 57.31 na ƙuri'un da aka kaɗa.
Ta doke 'yan takara 14 kuma nasarar da ta yi da fiye da kashi 50 cikin ɗari ta sa ba za a je zagaye na biyu na zaɓen ba.
“Kamar yadda Sashe na 109 na Kundin Zaɓe ya buƙata…ni, Elsie Nghikembua, shugabar Hukumar Zaɓe ta Namibia, ina ayyana Mai Girma Netumbo Nandi-Ndaitwah ta jam'iyyar SWAPO a matsayin wadda ta yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2024,” in ji Nghikembua a yayin da take sanar da sakamakon zaɓen a Windhoek, babban birnin ƙasar.
Nandi-Ndaitwah za ta kasance shugabar Namibia ta biyar kuma mace ta huɗu da ta zama shugabar ƙasa a Afirka bayan Ellen Johnson Sirleaf ta Liberia daga shekarar 2006 zuwa 2018; da Joyce Banda ta Malawi daga 2012 zuwa 2014; da kuma shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan.
Ta taɓa zama mataimakiyar shugaban jam'iyyar SWAPO lokacin da Hage Geingob ke jagorancinta. Daga bisani ya zama shugaban ƙasa sannan ya mutu a watan Fabrairun 2024 inda aka naɗa Shugaba Nangolo Mbumba domin ya kammala wa'adin mulkinsa.