Wannan ne karo na uku da Shugaba Ali Bongo Ondimba ya lashe zaben shugaban kasar. / Hoto: Reuters

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba ya sake lashe zaben shugaban kasar, a cewar sakamakon da hukumar zaben kasar ta fitar ranar Laraba.

Shugaba Bongo, wanda ya hau kan mulki shekara 14 da suka gabata, ya samu kashi 64.27 na kuri'un da aka kada a zaben da aka gudanar a makon jiya, a cewar hukumar zaben.

Wannan ne karo na uku da shugaban ya lashe zaben shugaban kasar.

Babban abokin hamayyarsa Albert Ondo Ossa, ya samu kashi 30.77 yayin da sauran 'yan takara 12 suka samu sauran kuri'in, in ji shugaban hukumar zaben Michel Stephane Bonda, a yayin da yake bayyana sakamakon zaben ta gidan talabijin na kasar.

Ya ce kashi 56.65 na mutanen da suka yi rajista ne suka fita kada kuri'unsu.

AFP