Janar Brice Oligui Nguema ya ce ba za su maimaita kura-kuran da aka yi a baya ba/ Hoto: AFP

Jagoran sojojin da suka kifar da gwamnatin shugaban kasar Gabon Ali Bongo ya ce yana so su guji yin gaggawar gudanar da zabe wanda zai sa "a maimaita kura-kuran da aka yi a baya".

Janar Brice Oligui Nguema ya bayyana haka ne ranar Juma'a a yayin da kasar ke shan matsin lamba don ta koma kan turbar dimokuradiyya.

Janar Nguema ya yi juyin mulki ne awanni kadan bayan hukumar zaben Gabon ta ayyana Bongo a matsayin mutumin da ya sake yin nasara a zaben shugaban kasar karo na uku.

Sojojin sun yi wa Bongo daurin-talala sannan suka nada Brice Oligui Nguema a matsayin shugaban kasar, abin da ya kawo karshen shekaru 56 da iyalan Bongo suka kwashe a kan mulkin kasar.

Juyin mulkin da aka yi a Gabon - wanda ya kasance na takwas da aka yi a Yammaci da Tsakiyar Afirka cikin shekaru uku - ya samu gagarumar tarba musamman daga mazauna babban birnin kasar Libreville, ko da yake an soke shi daga kasashen waje da ma wasu 'yan kasar.

Labari mai alaka: Brice Oligui Nguema: Tarihin sabon shugaban kasar Gabon

A wani jawabi da ya yi wa 'yan kasar ta gidan talabijin ranar Juma'a da maraice, Nguema ya ce za su yi hanzari wurin tabbatar da dawowar mulkin farar-hula amma ba za su "sake yin kuskuren" barin mutanen da suka dade a kan mulki su ci gaba da zama a kansa ba.

"Yin hanzari ba ya nufin za mu gudanar da zabe wanda zai kasance mai cike da irin kura-kuran da aka yi a baya," in ji shi.

Kungiyar kasashen Tsakiyar Afirka ECCAS ta yi kira ga kawayenta irin su Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka su goyi bayan mayar da tsarin mulki cikin hanzari, kamar yadda ta bayyana a wata sanarwa ranar Alhamis. Ta ce za ta gana ranar Litinin a kan lamarin na Gabon.

Ranar Juma'a babbar jam'iyyar hamayya a Gabon, Alternance 2023, wadda ta ce ita ce ta yi nasara a zaben makon jiya, ta yi kira ga kasashen duniya su lallashi sojoji su mika mulki a hannun farar-hula.

Reuters