'Yan Zimbabwe suna kada kuri'a a ranar Laraba a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki bayan kammala yakin neman zabe inda aka rika takura wa 'yan hamayya.
Akwai fargabar magudin zabe da kuma batun yadda mutane suka fusata kan tabarbarewar matsalar tattalin arziki.
Shugaba Emmerson Mnangagwa, mai shekara 80, wanda ya hau karagar mulki bayan juyin mulkin da ya yi wa marigayi Shugaba Robert Mugabe a shekarar 2017, yana neman yin ta-zarce.
Babban abokin hamayyarsa Nelson Chamisa, mai shekara 45, shi ne yake jagorantar jam'iyyar Citizens Coalition for Change (CCC), mai launin ruwan dorawa.
Yayin da yake kada kuri'arsa a garinsu mai suna Kwekwe a tsakiyar Zimbabwe, Mnangagwa ya shaida wa manema labarai cikin kwarin gwiwa cewa: "Idan na yi tunanin cewa ba ni ne zan yi nasara ba, to na yi shirme."
"Duk wanda ya shiga fafatawar, to ya yi haka ne don ya yi nasara," in ji shi.
Ana sa ran 'yan hamayya za su yi tasiri a zaben saboda yadda kasar wadda take yankin kudancin Afirka take fama da matsalar tattalin arziki ciki har hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi da kuma yadda talauci ya yi mata katutu.
A wata unguwa da ke wajen birnin Harare, mai suna Mbare, masu kada kuri'a sun yi layi da safiya a cikin wasu tantuna koraye wadanda aka ajiye akwatunan zabe a cikinsu.
Akwai wani bakin hayaki daga wata wuta da ke ci a wata kasuwa, hayakin yana kai wa ga wata rumfar zabe wacce aka yi jinkirin sa'a guda kafin a kai mata takardun kada kuri'a.
Yayin da rana take fitowa, wasu mutane sun yi amfani da fitilun wayoyinsu wajen neman sunayensu a takardun sunayen masu kada kuri'a da aka manna a bango a wajen tantunan.
Mutanen suna yin hakan ne don su tabbatar da cewa sun je rumfar zaben da ta dace da su.
Kafin mutane su kada kuri'arsu, jami'an zabe suna sanya musu tawada a yatsa don magance matsalar kada kuri'a sau biyu.
"Yana da muhimmanci na kada kuri'ata," in ji Diana Office, mai shekara 30 da wani abu.
Da aka tambaye ta ko tana da kwarin gwiwa abubuwa za su gyaru bayan zaben, sai ta yi dariya. "A'a". "Ina nan ne kawai don na sauke hakkina."
Batun canji ko kuma makoma mai kyau ana danganta su ne da magoya bayan Chamisa, wato jagoran 'yan hamayya.
Chamisa, lauya ne kuma malamin addinin Kirista ne wanda ya yi alkawarin samar da sabuwar kasar Zimbabwe "ga kowa da kowa" kuma ya yi alkawarin magance cin-hanci da rashawa da gyara tattalin arziki da dawo da kasar cikin jerin kasashen duniya, bayan da a baya aka mayar da ita saniyar-ware.