Hatsarin ya afku ne a daren Juma’a inda wata tirela da ke dauke da kaya da fasinja ta ƙwace wa direban a kan babban titin mai hada-hada.

Hukumar Kula da Kiyaye Afkuwar Hadurra ta Nijeriya FRSC ta tabbatar da mutuwar mutum 23, sannan wasu 50 sun ji raunuka a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a birnin Kano.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a ranar Juma’a ta ce hatsarin ya faru ne a gadar Muhammadu Buhari da ke babbar hanyar Kano zuwa Maduguri.

Kwamandan FRSC na shiyyar, Umar Mas’udu Matazu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce sama da mutane 50 sun samu raunuka, kuma yanzu haka suna samun kulawar likitoci a asibitin kwararru na Murtala Mohammed da kuma asibitin Abdullahi Wase da ke Kano.

Ya bayyana cewa, hatsarin ya afku ne a daren Juma’a inda wata tirela da ke dauke da kaya da fasinja ta ƙwace wa direban a kan babban titin mai hada-hada.

Kwamandan ya kuma ce, jami’an hukumar da na ‘yan sanda da kuma wasu ‘yan ƙasa nagari ne suka shiga tsakani domin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su tare da kawar da cunkoson da hadarin ya haifar domin cigaban zirga-zirgar ababen hawa.

TRT Afrika