Rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta ce ta kama mutum 93 kan zargin su da aikata miyagun laifuka a cikin kwanaki uku, daga jajiberi da ranar da kuma washe garin rantsar da sabon gwamnan jihar.
Dama tun kafin ranar rantsuwar rundunar ‘yan sandan ta fitar da sanarwa tana mai gargadin masu aikata miyagun laifuka da masu son ta da zaune tsaye da su kaurace wa filin wasanni na Sani Abacha, inda a can aka rantsar da sabon gwamnan.
A sanarwar da ta fitar a ranar Talata, 31 ga watan Mayu, rundunar ta ce "sai dai wasu sun ki jin shawarar sun zaci ba za mu aikata abin da muka fada ba, suka dauki gargadin a matsayin wasan yara."
Sanarwar ta ce kuma nan ba da jimawa ba za a kai su kotu.
“Ina da kwarin gwiwar cewa kotunanmu za su dauki matakin da ya dace da zai zama darasi ga masu niyyar aikata irin laifi a nan gaba,” a cewar mai magana da yawun rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya sanya hannu kan sanarwar.
Ga dai jerin wadanda ake zargin su da aikata laifukan da rundunar ta kama:
Kwacen waya
- An samu ayyuka 11 na masu kwacen waya da makami
- An kama mutum 56 da ake zargin su da laifin
- An kwato waya 18
- An kwato makamai 157.
Miyagun kwayoyi
- An samu laifukan tu’ammali da miyagun kwayoyi shida
- an kama mutum 17 da ake zargin su da aikata laifukan
- an kwace miyagun kwayoyi da suka hada da takarda biyar ta kwayar Tramadol
- leda 83 ta kwayar Diazepam
- sholisho 371
- wiwi kunshi 303
- da fakitin kwayar Extol 17.
Sauran miyagun laifuka da suka hada da satarababen hawa
- An samu ayyuka tara na masu satar abin hawa
- an kama mutum 20 da ake zargin su
- an kwato bindiga hudu kirar gida
- da mota biyu da babur biyu da talabijin biyu da janareto 34 da katin banki na cirar kudi ATM 34 da katan 23 na takin zamani.
Sanarwar ‘yan sandan ta ce a binciken farko-farko da rundunar ta fara gudanarwa ta gano kwararan hujjoji a kan wadanda take zargin na yadda suka zama masu son kawo cikas.
“Ko kuma aka dauki nauyin su don ta da zaune tsaye, musamman ganin yadda aka same su da muggan makamai kuma a buge da kayan maye da nufin yin fashi da kuma kawo tarnaki ga bikin rantsuwar gwamna da ake yi,” a cewar sanarwar.
Rundunar ‘yan sanda ta ce za a gurfanar da dukkan mutanen a gaban kuliya sannan ta ja kunne al’ummar jihar da su guji son tayar da hankali a ko ina suka samu kansu.