Gwamnatin Kano ta zargi Ganduje da sayar da filaye ba bisa ka'ida ba. Hoto/Facebook Abdullahi Ganduje

Tsohon gwamnan Kano da ke Nijeriya, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ya kai wa shugaban kasar Bola Tinubu korafi game da yadda sabuwar gwamnatin jihar take ta rushe-rushe.

Ya bayyana haka ne ga manema labarai ranar Juma'a a fadar shugaban kasar jim kadan bayan ya gana da shi.

A ranar 29 ga watan Mayu Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP ya maye gurbin Ganduje a matsayin gwamnan Kano kuma tun daga lokacin gwamnatinsa take rusa wasu gine-gine da ta ce an yi su ba bisa ka'ida ba.

Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a ciki da wajen jihar, inda wasu ke goyon bayan matakin yayin da wasu ke korafi.

Sai dai a ranar Juma'ar nan, tsohon gwamna Ganduje ya je fadar shugaban kasar don shigar da kokensa kan lamarin a daidai lokacin da shi ma tsohon gwamnan na Kano Rabiu Kwankwaso ya je fadar inda ya gana da Shugaba Tinubu.

Ganduje ya shaida wa manema labarai cewa "idan ba za mu iya mutunta ayyukan da gwamnatin da ta gabata ta yi, mu ce abin da ta yi ba ya kan ka'ida ba tare da mun yi nazari a kansa ba, ta yaya za mu gudanar da gwamnati a wannan salo?"

Ya kara da cewa mutane suna zagin gwamnati a kan rusau din da take yi, yana mai ikirarin cewa hakan ya shafi har ma masu goyon bayanta.

"Wannan batu shi ne ya kawo ni wurin shugaban kasa kuma na yi masa cikakken bayani a kan haka. Na tura wa babban sifeton 'yan sanda bidiyon (rusau da ake yi), yana sane da hakan," in ji Ganduje.

Tsohon gwamnan ya ce yana sane cewa Kwankwaso yana cikin fadar shugaban kasa "kuma watakila da mun hadu da shi da na mare shi."

'Babu wanda zai lamunci barnar da Ganduje ya yi'

Sai dai a nasa bangaren, Sanata Kwanwaso, ya shaida wa maneman labarai cewa Shugaba Tinubu ne ya gayyace shi fadarsa domin tattaunawa kan batutuwa daban-daban.

Ya ce "mun tattauna da shugaban kasa kan yadda za a ciyar da Nijeriya gaba kuma mun tattauna abubuwa musamman ma na Kano.

Maganar da take fitowa daga Kano, wadanda ba su san sirrin ba sai su dauka wani abu ake yi na cutar da wasu. Amma wannan abin da muke yi shi muka yi kamfen da shi har jama'a suka zabe mu."

Kwankwaso ya kara da cewa babu wani mai daraja da zai kyale barnar da Ganduje ya yi ba tare da an gyara ba, yana mai cewa "daya daga cikin wuraren da aka rusa, Filin Sukuwa na gwamnati ne, amma an bai wa dansa (Ganduje). Muna ganin wannan bai dace ba."

TRT Afrika