Hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali ta Jihar Kano a arewacin Nijeriya ta ce mutum dari da arba'in ne suke jira a zartar musu da hukuncin kisa bayan kotuna sun same su da laifuka.
Kakakin hukumar, Musbahu Kofar-Nassarawa ne ya bayyana haka ranar Asabar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, News Agency of Nigeria (NAN) ya rawaito.
Ya kara da cewa mutanen sun hada da maza da mata.
"Hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali ta Kano ba ta da mai rataye mutane saboda wuri ne na daure mutanen da suka aikata matsakaitan laifuka," in ji Kofar-Nassarawa.
Ya kara da cewa gwamnonin da suka mulki jihar sun gaza sanya hannu a takardun zartar da hukuncin kisa ko kuma su mayar da hukuncin na daurin rai-da-rai.
“Wasu gwamnonin suna amfani da damar da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba su domin sakin mutanen da ke kurkuku bisa samun shawarwari daga Majalisar Bayar Da Shawara kan yi wa fursunoni afuwa domin rage cunkoso a gidajen yari," a cewar Musbahu Kofar-Nassarawa.