Akalla mutum 10 ne suka mutu bayan motarsu ta taka nakiyoyi a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya, kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar ranar Talata.
Lamarin ya faru ne a yankin Gamboru da ke kan iyakar Nijeriya da Kamaru, in ji kamfanin dillanacin labarai na AFP, wanda ya ambato mazauna yankin.
Ranar Talata da safe, mutum bakwai sun mutu lokacin da motar a-kori-kura da suke ciki mai dauke da mutum tara ta taka wata nakiya da ake zargin ‘yan ta’adda sun binne a kauyen Kunibaa da ke kusa da Gamboru, a cewar wasu majiyoyi.
"Motar ta kama da wuta bayan ta taka nakiya a wani wuri mai nisa kilomita 15 daga Gamboru, inda mutum bakwai suka mutu," in ji Shehu Mada, wani shugaban ‘yan bijilante da ke Gamboru.
Mutum biyu sun jikkata, a cewar Usman Hamza, shi ma wani jami’in kungiyar bijilante.
Cikin wadanda suka mutu har da wata mata da ‘ya’yanta biyu wadanda ke kan hanyar zuwa Maiduguri domin halartar biki, kamar yadda Babandi Abdullahi, wani mazaunin Gamboru ya ce.
Babandi ya ce ya halarci jana’izar matar da ‘ya’yana da kuma mutum na hudu da yam utu ranar Talata da rana.
Ranar Litinin, wasu mutum uku sun mutu lokacin da wata karamar mota da motar a-kori-kura suka taka nakiliyoyi a kan hanyarsu ta zuwa Gamboru.
"Direban karamar motar da fasinjoji biyu sun mutu yayin da sauran suka jikkata, ciki har da wanda aka yanke wa kafa," in ji Umar Kachalla, shugaban ‘yan bijilante.
Kachalla ya kara da cewa jami'an tsaro da ke sintiri a kan hanyar ne suka kwance sauran nakiyoyin da aka binne.