Ranar Laraba, ɗaruruwan mutane, ciki har da masu yawan buɗe ido kusan 100 sun maƙale a fitaccen gandun dabbobi Maasai Mara bayan an tafka ruwa a yankin./Hoto:AFP

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Kenya ranar Alhamis ta ce mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwan da ta auka wa ƙasar sun kai 188, a yayin da ake ci gaba da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.

Sassa daban-daban na ƙasar da ke Gabashin Afirka suna ci gaba da fuskantar ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa, lamarin da ya haddasa rushewar gadaje da gine-gine.

"Abin takaici shi ne, mutum 188 sun mutu sakamakon iftila'in ambaliyar ruwa," in ji sanarwar da ma'aikatar ta fitar.

Ta ƙara da cewa mutum 125 sun jikkata sannan mutum sama da 90 sun ɓata, yayin da ambaliyar ruwan ta raba aƙalla mutum 165,000 da muhallansu.

Aikin ceto

Alal misali, gomman mutane sun mutu lokacin da wata madatsar ruwa ta yi ambaliya a ƙauyen Mai Mahiu na kusa da Kwazazabon Rift Valley, mai nisa kilomita 60 daga Nairobi.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan ta ce an gano gawawwaki 52 yayin da mutum 51 suka ɓata bayan madatsar ruwan ta fashe.

Ranar Laraba, ɗaruruwan mutane, ciki har da masu yawan buɗe ido kusan 100 sun maƙale a fitaccen gandun dabbobi Maasai Mara bayan an tafka ruwa a yankin.

Ma'aikatar ta ce masu aikin ceto sun kuɓutar da aƙalla mutum 90 daga Masai Mara, inda gidaje 19 da masu yawon buɗe idanu suka maƙale bayan Kogin Talek ya yi ambaliya.

AFP