Rundunar 'yan sandan Kano da ke Nijeriya ta ce jami'an tsaro sun gano wasu mutane da ke shirin tayar da hargitsi a jihar tare da kai hari wasu muhimman wurare ciki har da Majalisar Dokokin jihar.
Kwamishinan 'yan sanda jihar Muhammad Hussaini Gumel ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai bayan wata ganawa kan al'amuran tsaro a Gidan Gwamnatin Kano ranar Lahadi da daddare.
Ya ce sun samu wasu bayanai na tsaro dangane da wasu gungun mutane "da ake ɗaukar su maƙiyan jihar, 'yan daba waɗanda suke ƙoƙarin ƙaddamar da ta'addanci a jihar ta hanyar kai hare-hare a wasu zaɓaɓɓun wurare, musamman Majalisar Dokokin jihar da wasu fitattaun wurare a babban birnin jihar."
Gumel ya ce sun samu labari a cikin daren da ya gabata cewa wasu "suna so su fara ƙona tayoyi su ta da hankalin mutane yadda za a sauya wa Kano suna, a ce akwai hargitsi, akwai tashin hankali."
Kwamishinan ya ƙara da cewa duk wanda yake so ya gwada ƙwanjinsa, to hukumomin tsaro suna da ƙarfin da za su iya rufe ido su koya wa waɗannan maƙiyan na jihar hankali.
"Don haka a daren nan ina sanar muku cewa mun yi kyakkyawan shiri wajen fara wani sintiri na gaske tare da gano - musamman - wuraren da muka samu ingantattun bayanan sirri cewa, waɗannan maƙiyan jihar suna ɓuya," a cewar Kwamishinan 'yan sandan Muhammad Gumel.
Ya ƙara da cewa duk inda mutanen suka shiga sai sun zaƙulo su.
Ya bayyana cewa duk wanda yake so ya yi amfani da saɓanin da aka samu tsakanin masarauta da gwamnati domin tayar-da-zaune-tsaye to ba za a ƙyale shi ba, za a zaƙulo shi, da wanda ya tsaya masa a gurfanar da su gaban shari'a.
"Za mu fara bincike gida-gida don kamo duk wani mutum da yake ganin ya fi ƙarfin dokokin jihar," a cewar Kwamishinan.
Kwamishinan ya kuma ƙara da cewa an jibge jami'an tsaro a duka fadojin masarautu da kuma Majalisar Dokokin jihar.
Ya ƙara da cewa Kano za ta ci gaba da zama cikin lumana, kuma babu wanda ya isa ya kawo matsala ga zaman lafiyar da ake da shi a jihar.
A ranar Lahadi ne wasu mutane suka gudanar da zanga-zanga a kusa da gidan Sarki na Nasarawa har ma suka ƙona tayoyi, yayin da suke kira a mayar da Alhaji Aminu Ado Bayero sarautar Kano.
Sai dai Kwamishinan 'yan sandan ya ce wasu 'ɓata-gari' ne suka so su yi amfani da sunan masu goyon bayan Aminu Ado Bayero wajen ta da hargitsin, amma ya ce duka-duka ba su wuce minti goma ba suka watse, "tun ma kafin 'yan sanda su je wajen."
An kuma samu rahotannin makamanciyar wannan zanga-zangar a masaratun Gaya da Bichi.
Tun ranar Asabar ne dai aka shiga zaman ɗar-ɗar a Kano bayan komawar Alhaji Aminu Ado Bayero birnin, kwana ɗaya bayan Gwamna Abba Kabir ya sanar da sauke duka sarakunan jihar biyar, ya kuma mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.
"Batun harkar masarauta harumi ne na ɓangaren zartarwa. Wajen da za ka warware duk wata rashin amincewa shi ne kotu," kamar yadda Kwamishinan ya bayyana.
"Gobe Litinin, an san Kano da kasuwanci, za a buɗe makarantu, za a buɗe bankuna, za a buɗe kasuwanni. Muna da isassun jami'ai da za su yi sintiri a birnin, kada jama'a su ji tsoron komai," in ji shi.