Gobarar wadda aka yi a watan Agusta ta kashe akalla mutum 76. / Hoto: Reuters

Daga Charles Mgbolu

A tsakiyar wata unguwa da ke birnin Johannesburg, a gundumar Marshalltown, akwai wani gini mai hawa biyar wanda ke kan wani titi da ke cike da hada-hada.

Mutane kan wuce ta gaban ginin suna rawar jiki yayin da suke kallon ginin, wanda ke da lamba ta 80 a kan titin Albert.

Akalla mutum 76 suka mutu a cikin ginin, inda wasu gommai suka samu raunuka, a lokacin da wata mummunar gobara ta tashi a ranar 31 ga watan Agusta.

Wadanda suka rasa rayukansu akasarinsu ba su da matsuguni, daga ciki har da yara 12, sun makale a cikin ginin a lokacin da gobarar take ci inda ta cinye ginin.

Kofar tsira wadda aka tanada saboda gobara ta kasance a kulle da sarka, haka kuma sauran kofofin ficewa cikin gaggawa sun kasance a rufe, babu wani wurin tserewa.

Sauran mutanen da ke ciki wadanda hayaki ya turnuke sun kone da wutar, wanda hakan ya sa suka mutu.

An bayyana wannan gobarar a matsayin daya daga mafi muni a tarihin Afirka ta Kudu, inda Shugaba Ramaphosa ya kira ta da gobara "mai sakawa a farka."

Wannan bala'in ya kasance wata tunatarwa ga wata matsala wadda ake fama da ita amma an yi shiru.

Gine-ginen da suka cika da jama'a

Akwai daruruwan gine-gine a Johannesburg da suka cika makil da jama'a, da ba a saka ido a kai kuma akasarinsu mutane ne wadanda ba su da karfi ke zaune a ciki da 'yan ci-rani wadanda ba su da takardun zama.

Kungiyoyi masu zaman kansu wadanda suka dakile yunkurin da aka yi na fitar da wadannan mutanen daga irin gine-ginen, an dora alhakin faruwar wannan lamarin a kansu.

Wadannan kungiyoyin masu zaman kansu sun yi amfani da wata doka ta Afirka ta Kudu mai suna South Africa's Prevention of Illegal Eviction Act (PIE Act), wadda ta ce babu wani wanda za a iya fitarwa daga gidan da yake zaune ba tare da umarnin kotu ba.

Haka kuma dokar ta bayyana karara cewa da zarar mutum ya zauna a cikin gida kuma zai iya tabbatarwa da cewa babu wani wurin da zai iya zuwa, ba za a iya korar shi daga gidan ba. Hakan ne ya sa fitar da mutane daga gine-gine ciki har da irin wanda wannan lamarin da ya faru ya kasance lamari mai wahala.

Bayan faruwar wannan lamari, daya daga cikin jami'an Johannesburg Mgcini Tshwaku ya bayyana cewa gidan da aka yi gobarar na daga cikin gine-gine sama da 600 a birnin da ake zaune ba bisa ka'ida ba ko kuma - "aka mamaye."

'Yan ci-rani a cikin gine-gine

Irin wadannan gine-ginen, akasarinsu 'yan ci-rani wadanda suka shiga Afirka ta Kudu ba bisa ka'ida ba ke zaune a ciki, wadanda suka fito daga kasashe kamar su Nijeriya da Somalia da Zimbabwe domin neman rayuwa mai inganci.

A makonnin karshe na 2023, dakarun da ke kula da iyakokin Afirka ta Kudu sun kara matsa kaimi domin tare motocin da ke dauke da 'yan ci-rani wadanda ke kokarin shiga kasar, akasarinsu ta iyakar Zimbabwe.

Hukumomi sun bayyana cewa matakin farko ne na dakile karuwar masu shiga kasar ba bisa ka'ida ba.

Sai dai idan aka yi la'akari da gobarar da aka yi, da kuma yiwuwar samun karin mace-mace a wasu gine-gine irin su, akwai tambayoyi da dama da ke bukatar amsa.

Shugaba Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa yana da muhimmanci ga gwamnati ta magance wannan matsalar.

Sai dai masu sharhi da dama suna nuna damuwa kan cewa kalaman na shugaban kasar ba su fito karara sun yi bayani kan yadda za a magance matsalar ba.

A yayin da ginin mai lamba 80 da ke kan titin Albert ke ci gaba da zama wurin da yake bayan gobara ta lalata shi, 'yan Afirka ta Kudu na sa ran cewa ba za a manta da kukan mutum 76 wadanda suka rasa rayukansu ba, da kuma irin kalubalen da 'yan ci-rani wadanda suke zaune ba bisa ka'ida ba ke fuskanta

TRT Afrika