Adadin mutanen da suka mutu sanadin ambaliyar ruwan a birnin Derna ya karu zuwa 5,300, kamar yadda mahukunta a yankin suka bayyana. / Hoto: AFP

Dubban mutane ne suka bace a birnin Derna sanadin ambaliyar ruwa da mahaukaciyar guguwa da aka yi lakabi da Daniel ta jawo a kasar Libya.

Adadin mutanen da suka mutu sanadin ambaliyar ruwan a birnin Derna ya karu zuwa 5,300, kamar yadda mahukunta a yankin suka bayyana.

"Akalla mutum 5,300 ne suka mutu a birnin Derna kadai," kamar yadda Tareq al-Kharaz wani mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida a Yankin Gabashin Libya ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

Ya ce an binne akalla gawawwaki 1,300 bayan daginsu sun gane su.

"Tun da farko iyalai sun tarwatse saboda mummunar bala'in da iska mai karfi ta jawo," in ji al-Kharaz. "Ba za a iya gane gawawwaki ba kuma an kasa binne su."

Mai magana da yawun ya ce ana saran adadin wadanda suka mutu ya haura 10,000 a daidai lokacin da abubuwan more rayuwa suka lalace a birnin.

Hukumar ceton gaggawa ta Libya tun da farko ta ce adadin wadanda suka mutu daga ambaliyar ruwan a birnin Derna ya kai 2,300 kuma akwai mutum 5,000 da suka bace.

Hukumar Agaji ta Duniya (ICRC) a ranar Talata ta ce fiye da mutum 10,000 ne ake da rahoton cewa sun bace bayan mummunar ambaliyar ruwa a Libya.

Rahotannin farko sun ce ambaliyar ta ci kauyuka da garuruwa wadda guguwa wacce aka wa lakabi da Daniel da ta fada gabashin Libya ta jawo a ranar Lahadi.

Mahukunta a yankin Derna sun ce dam biyu ne suka balle a birnin, abin da ya kara munin al'amarin.

"Hanyoyin mota da gadoji sun ruguje gaba daya a Derna," in ji Al-Hussein Sweidan shugaban hukumar da ke kula da hanyoyi da gadoji a bangaren gwamnatin Tripoli.

Ya yi hasashen za a kashe miliyan 300 na dinar din Libya (dala miliyan 67 kenan) wajen sake gina hanyoyi da gadoji.

A ranar Litinin gwamnatin Libya ta mika kokon baranta ga kasashe kawayenta da kungiyoyin bayar da agaji a duniya da su taimaka mata da kayan agaji a yankin gabashin kasar.

AA