Akalla mutum 1,305 ne suka mutu sakamakon mummunar girgizar kasar da ta faru a Maroko ranar Juma’a, a cewar ma'aikatar cikin gida ta kasar.
Ta kara da cewa mutum 1,220 ne suka jikkata sakamakon girgizar kasar mai karfin maki 7.0 da ta kassara yankuna da dama na kasar.
Girigizar kasar ta kuma lalata gine-gine yayin da mutane suka rika tserewa daga gidajensu cikin firgici.
"Rahoton wucin-gadi ya nuna cewa girgizar kasar ta kashe mutum 296 a larduna da biranen al-Haouz, Marrakesh, Ouarzazate, Azilal, Chichaoua da kuma Taroudant," in ji sanarwar, wadda ta kara da cewa an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti.
Wasu bidiyoyi da aka rika watsawa a shafukan sada zumunta wadanda ba a tantance sahihancinsu ba sun nuna yadda gine-gine suka rika rushewa yayin da wasu suke girgiza. An ga mutane cikin dimuwa yayin da wasu suke fitowa daga baraguzan gine-gine.
"Mun ji wata mahaukaciyar girgiza. Daga nan na fahimci cewa girgizar kasa ce. Mutane sun fada cikin firgici da yamutsi. Yara suna ta kuka yayin da iyaye suka dimauce," kamar yadda Abdelhak El Amrani, wani mazaunin Marrakesh ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP ta wayar tarho.
Hukumar da ke nazari kan girgizar kasa ta Amurka [USGS] ta ce bayanan farko sun nuna cewa girgizar kasar da ta auku a Maroko tana da karfin maki 6.8 kuma ta faru a nisan kilomita 18 daga karkashin kasa.
Ta ce girgizar kasar ta faru ne da misalin karfe 11:11 na dare a agogon kasar kuma ta fi kamari a yanki mai fadin kilomita 56.3 a yammacin Oukaimeden, fitaccen wurin yin wasan zamiya da ke Tsaunukan Atlas.
Kafofin watsa labaran Maroko sun ce girgizar kasar ita ce mafi karfi da kasar ta taba fuskanta a tarihinta.
An ji karar girgizar kasar a Algeria da ke makwabtaka da Maroko, ko da yake Jami'an Tsaron Algeria sun ce ba ta yi wata barna ba.
A 2004, akalla mutum 628 ne suka mutu yayin da 926 suka jikkata sakamakon girgizar kasar da ta auku a Al Hoceima da ke arewacin Maroko.