Shigar Kungiyar Tarayyar Afirka AU jerin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki na duniya wato G20 babbar amincewa ce ga Afirka ganin cewa tana da kasashe sama da 50 wadanda suke son taka rawa a idon duniya.
A bara ne shugaban Amurka Joe Biden ya bukaci a bai wa AU matsayin mamba ta dindindin a G20.
Firaiministan Indiya Narendra Modi a ranar Asabar ya sanar da cewa an gayyaci kungiyar ta shiga taron na G20 wanda kasarsa ke karbar bakunci.
Kungiyar Tarayyar Afirka na ta son zama cikakkiyar mamba a kungiyar tsawon shekaru bakwai, kamar yadda mai magana da yawun kungiyar Ebba Kalonda ya bayyana.
Zuwa yanzu, Afirka Ta Kudu ce kadai mamba a kungiyar daga kasashen Afirka.
Bari mu duba wasu abubuwa kan AU da kuma abin da zamanta mamba ke nufi a duniyar da Afirka ta kasance abar magana ta fannin matsalolin sauyin yanayi da karancin abinci da ci-rani da sauran matsaloli.
Me wannan yake nufi ga Afirka?
Zamanta mamba ta dindindin a G20 wata alama ce ta samun ci-gaba a nahiya da ke da jama’a kusan biliyan 1.3 kuma ana sa rai adadin zai ninka nan da 2050, inda za ta zama ita ke da daya bisa hudu na jama’ar duniya.
AU, wadda ke da mambobi 55, ciki har da Yammacin Sahara da ake rikici a kai, na ta matsa kaimi domin samun dama mai kyau a kungiyar kasashen duniya daban-daban ciki har da Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya.
Haka kuma suna son sauyi a tsarin kudi na duniya – ciki har da Bankin Duniya da sauran bangarori.
Afirka na ƙara kara samun masu son saka hannun jari da sha'awar kawance sabbin manyan ƙasashen duniya fiye da Amurka da ƙasashen da suka yi wa nahiyar Turai mulkin mallaka.
China ta kasance kasa mafi girma da ta fi kasuwanci da Afirka kuma ita ce kasar da ta fi ba ta bashi. Rasha a dayan bangaren ta kasance kasar da ta fi samar mata da makamai.
Sai kuma kasashen yankin Gulf sun kasance kasashen da suka fi zuba jari a nahiyar. Sansanin soji da ofishin jakadanci mafi girma na Turkiyya duk suna a Somaliya.
Labari mai alaka: Tarayyar Afirka ta zama sabuwar mamba a kungiyar kasashen G20
Isra’ila da Iran na kara fadada hannayensu domin neman abokai. Shugabannin na Afirka sun kalubalanci yadda ake nuna nahiyar a matsayin wadda ke fama da yaki da tsatsauran ra’ayi da yunwa da bala’i wanda ya sa kasashen ke daukar bangare daga cikin kasashen Yamma.
Wasu kasashen sun fi son zama masu shiga tsakani, kamar yadda aka ga Afirka na kokarin sasanci bayan yakin Rasha da Ukraine ya barke. Bai wa AU mamba a G20 wani mataki ne wanda ya nuna cewa nahiyar ta zama wata babbar mai fada a ji a duniya ita ma.
Wacce gudunmawa AU za ta bai wa G20?
Ganin cewa ta zama cikakkiyar mamba ta G20, AU za ta iya wakiltar nahiyar da ke da kasashe mafi yawa da ke cinikayya maras shinge.
Haka kuma nahiyar tana da matukar ma’adinai da duniya ke bukata domin yakar sauyin yanayi, wadda Afirka nahiya mafi karanci wurin bayar da gudunmawa wurin tabarbarewar yanayi amma ita lamarin ya fi shafa.
Nahiyar Afirka ce ke da kashi 60 cikin 100 na makamashi maras gurbata muhalli da kuma sama da kaso 30 cikin 100 na muhimman ma’adinai wadanda ake amfani da su wurin makamashi maras gurbata muhalli.
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo kadai tana da kusan rabin sinadarin cobalt wanda ake bukata, wanda karfe ne mai muhimmanci wanda ake batirin lithium da su, kamar yadda rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana a wani rahoto da ta saki a watan da ya gabata.
Shugabannin Afirka sun gaji da ganin wasu daga kasashen waje suna kwashe ma’adinai daga kasashe suna kaiwa wasu wuraren domin sarrafawa suna samun riba inda suke son a kara samun kamfanonin sarrafa su a kusa da su.
Idan aka yi la'akari da kadarorin Afirka za a ga cewa nahiyar na da dumbin arziki, in ji shugaban kasar Kenya William Ruto a wajen taron sauyin yanayi na Afirka na farko.
Taron da aka yi a Nairobi ya kare da yin kira ga cibiyoyin hada-hadar kudi, su yi adalci da isar da dalar Amurka biliyan 100 da kasashe masu arziki suka dade suna yi wa kasashe masu tasowa alkawari duk shekara domin yaki da sauyin yanayi da kuma saka haraji kan makamashi mai gurbata muhalli
Samun matsaya guda a tsakanin kasashen kungiyar ta AU, tun daga masu karfin tattalin arzikin irin Nijeriya da Habasha zuwa wasu kasashe mafi talauci a duniya, na iya zama kalubale.
Kuma ita kanta kungiyar AU wasu ‘yan Afrika sun dade suna ba ta shawarar ta kara kaimi wajen tunkarar juyin mulki da sauran rikice-rikice.
Shugabancin karba-karba na kungiyar, wanda ke ake sauyawa kowace shekara, shi ma yana kawo cikas ga daidaito, amma akwai bukatar Afirka "yin magana da murya daya idan har tana fatan yin tasiri wajen yanke shawarar a taron G20,"in ji Ibrahim Assane Mayaki, tsohon Firaiminista na Nijar, da kuma Daouda Sembene, tsohon daraktan zartarwa na Asusun Ba da Lamuni na Duniya, a wata makala da suka rubuta a bana.
Yanzu a matsayinta na babbar kasa a G20, zai yi wuya a rinka watsi da bukatun Afirka