Binciken ya gano cewa kashi 85 na likitoci mata masu kasa da shekara 40 ba su taba yin gwajin cutar kansa ba. /Hoto Ghana News Agency

Wani bincike ya nuna cewa mata ma'aikatan lafiya a kasar Ghana suna boye kullutun da ke fitowa a kan mama da ke nuna alamun kamuwa da cutar daji kuma ba sa bari a yi musu gwajin cutar.

An gudanar da binciken, wanda a turance aka yi wa taken 'Knowledge, Attitude and Breast Cancer Practices Screening among female nurses in a Tertiary Hospital in Ghana' a 2022, a cewar kamfanin dillancin labarai na Ghana News Agency.

Binciken ya nuna cewa kashi 60 na mata masu aikin nas sun yarda cewa ba za su amince a yi musu tiyatar cire mama ba idan suka kamu da cutar daji.

Ya kara da cewa duk da ilimin da suke da shi a kan cutar, kashi 67 ne na likitoci mata suke yin gwajin cutar daji a-kai-a-kai, kashi 39 sun taba yin gwajin a baya sannan kashi 85 na likitoci mata masu kasa da shekara 40 ba su taba yin gwajin cutar kansa ba.

Dr Afuah Commeh, babbar jami'a da ke sanya ido kan cutaka marasa yaduwa a Ghana, wadda ita ce ta bayar da wadannan alkaluma, ta ce wannan bincike abin takaici ne domin kuwa ya kamata nas-nas su ilimantar da mutane kan muhimmancin yin gwajin cutar kansa.

Ta bayyana haka ne a wuron wani taro kan yadda za a dakile cutar daji a kasar.

Dr Commeh ta ce binciken na 2022 ya nuna cewa mata 4000 ne suka kamu da cutar kansa a kasar sannan 2000 daga cikinsu sun mutu sakamakon rashin zuwa a yi musu gajin cutar da wuri.

"Abu ne da bai kamata ba a ce fiye da kashi 50 na matan da aka gano dauke da cutar daji suna mutuwa kuma na yi amanna wannan adadi ya zarta haka domin ba a gano wasu," in ji ta.

TRT Afrika