Jama'a da dama a Kenya sun fito zanga-zanga a Kenya a ranar Talata inda suka kutsa majalisar dokokin Kenya, lamarin da ya ja akalla mutun guda ya rasa ransa a yau.
Masu zanga-zangar sun fito ne domin nuna rashin jin daɗinsu dangane da ƙarin harajin da aka yi a ƙasar, inda suka shafe kusan mako guda suna bore, lamarin da ke son zama ƙarfen ƙafa ga gwamnatin ƙasar.
Matasan na Kenya na jin cewa dama tuni 'yan ƙasar na biyan haraji mai yawa, inda suke cewa ba za su iya biyan sabon harajin da aka saka za su biya a sabon kasafin kuɗin ƙasar ba.
'Yan sanda masu kwantar da tarzoma sun rufe majalisar ƙasar da ke Nairobi babban birnin ƙasar, wanda a nan ne 'yan majalisar ƙasar za su zauna su tattauna kan kasafin kuɗin ƙasar wanda ke son ƙara haraji da dala biliyan 2.7.
Zuwa yanzu rahotanni sun ce aƙalla mutum takwas suka rasa ransu a ƙasar tun bayan soma zanga-zangar.
Shugaba William Ruto ya ci zaɓe shekara biyu da suka gabata inda ya yi alƙwarin ƙwato wa ma'aikata haƙƙinsu. A halin yanzu ya bayyana cewa tsananin bashin ƙasar wanda kuɗin ruwansa a halin yanzu yake lashe kaso 37 cikin 100 na kuɗin shigar ƙasar ya hana shi cika alƙawarin da ya ɗauka.
A halin yanzu ya shiga tsaka mai wuya a tsakanin bukatun masu bayar da bashi kamar su Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF, wanda ke kira ga gwamnati da ta rage gibi, da kuma ƙara haraji ga al’ummar da ke fama da tsadar rayuwa sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.
Dubban mutane sun shiga kan titunan Nairobi inda sama da birane 12 a ƙasar su ma jama'a sun fito zanga-zanga a makon da ya gabata.
Duk da cewa masu zanga-zangar na Nairobi daga farko suna yin ta ne a cikin lumana, kamfanin dillancin labarai na Reuters da ƙungiyoyin kare haƙƙi sun nanata cewa 'yan sanda sun ta hatba hayaƙi mai sa hawaye da kuma fesa ruwan zafi.