Hedkwatar Tsaron Nijeriya ta yi zargin cewa masu shirin gudanar da zanga-zanga a ƙasar suna so ne su mayar da ita tarzoma kamar yadda ya faru a ƙasar Kenya inda aka kashe mutane da dama tare da ƙone-ƙone.
Mai magana da yawun Hedkwatar Tsaron Nijeriya Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudanar ranar Alhamis a Abuja, babbar birnin ƙasar.
Manjo Janar Buba ya ce duk da yake 'yan Nijeriya suna da 'yancin yin zanga-zangar lumana, amma sojoji ba za su lamunci duk wani taro da zai rikiɗe zuwa tarzoma ba.
Ya ƙara da cewa rundunar tsaron ƙasar ta bankaɗo shirye-shiryen da wasu marasa kishin ƙasa suke yi na yin amfani da zanga-zangar domin kai hare-hare kan 'yan Nijeriya da ba su ji ba ba su gani ba da kuma harkokin kasuwanci.
“Yayin da 'yan ƙasa suke da 'yancin yin zanga-zangar lumana, ba su da 'yancin tayar da tarzoma,” in ji Janar Buba.
Ya ce, “Wannan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa, za a yi ta ne salon abin da ke faruwa a Kenya kuma ina so na ce, na ɗaya, abin da ke faruwa a Kenya tarzoma ce, sannan na biyu, a yayin da mke wannan magana, ba a warware rikicin ba."
“A nata ɓangaren, Rundunar Tsaron Nijeriya ba za ta naɗe hannu ta ƙyale a gudanar da tarzoma ba a ƙasarmu ba. Domin kuwa mun ga yaƙe-yaƙe kuma mun ga yadda tarzoma ta ɓarke a ƙasashen da muka kai wa ɗauki, musamman na rundunar ECOMOG (Economic Community of West African States Monitoring Group) da kuma yadda muka yi aikin wanzar da zaman lafiya a wasu ƙasashe," a cewar Janar Buba.