Mali ta karɓi sabbin kayan yaƙin da ta sayo daga Turkiyya domin murƙushe 'yan ta'adda

Mali ta karɓi sabbin kayan yaƙin da ta sayo daga Turkiyya domin murƙushe 'yan ta'adda

Kayan yaƙin sun haɗa da jirgi mara matuƙi mai suna AKINCI, wanda kamfanin Turkiyya, Baykar, ya ƙera da aka fi sani da TB2.
Shugaban mulkin sojin Mali, Janar Assimi Goita, ya miƙa sabbin kayan yaƙin ga Rundunar Sojojin Mali (FAMa) a Bamako ranar Talata, ta hannun Ma'aikatar Tsaro da 'Yan Mazan-Jiya./Hoto: Others

Ƙasar Mali ta sayi sabbin kayan yaƙi daga Turkiyya, ciki har da jirage marasa matuƙa, domin ƙarfafa yaƙin da take yi da ƙungiyoyin 'yan ta'adda.

Shugaban mulkin sojin Mali, Janar Assimi Goita, ya miƙa sabbin kayan yaƙin ga Rundunar Sojojin Mali (FAMa) a Bamako ranar Talata, ta hannun Ma'aikatar Tsaro da 'Yan Mazan-Jiya, a cewar gidan talbijin na ƙasar.

Waɗannan kayan yaƙi na zamani za su ƙarfafa fafutukar da ƙasar take yi wajen kawar da 'yan ta'adda tare da inganta tsaronta, a cewarsa.

Kayan yaƙin sun haɗa da jirgi mara matuƙi mai suna AKINCI, wanda kamfanin Turkiyya, Baykar, ya ƙera da aka fi sani da TB2.

Bayar da fifiko

Ministan Tsaron Mali, Janar Sadio Camara, ya yi maraba da wannan ƙoƙari, inda ya ce: "Amfani da kasafin kuɗi waje sayen waɗannan sabbin jirage zai buɗe mana sabuwar hanya. Za su taimaka mana wajen tsaron ƙasa tare da kawar da 'yan ta'adda."

"Hukumomin Mali sun bayar da da fifiko wurin dawo da tsaron ƙasar sakamakon ci gaba da suke yi da sauraren buƙatun al'umma," in ji Janar Camara.

Ministan Tsaron ya ƙarfafa gwiwar dakarun tsaro domin su yi aiki da waɗannan kayan yaƙi yadda ya kamata wajen biyan buƙatun al'ummar Mali waɗanda ke fama da hare-haren Abzinawa 'yan a-aware da sauran ƙungiyoyin 'yan ta'adda.

Ƙara yauƙaƙa dangantaka

Wani sojan Mali ya bayyana jirgin yaƙin a matsayin "ainahin jirgin yaƙi", da kuma bayyana yaƙininsa kan jirgin bayan kai kayayyakin.

"Sakamakon yana da fasahar optronic balls, jirgin maras matuƙi na AKINCI na gani da rana da dare, inda zai iya zagawa duka ƙasar," in ji sojan.

Yadda Turkiyya ke ƙara yauƙaƙa dangantaka da yankin na Sahel, musamman Nijar da Mali da Burkina Faso ya sa an samu ƙaruwar tattalin arziƙi da kuma dangantakar soji.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashe da dama a yankin suka yanke alaƙa da ƙasashen Yamma musamman Faransa wadda ita ce uwar goyonsu, inda suka bayyana Turkiyya a matsayin wadda za a su iya dogara da ita.

TRT Afrika