Mali, Burkina Faso da Nijar na binciken ɗan jaridar Faransa kan ta'addanci

Mali, Burkina Faso da Nijar na binciken ɗan jaridar Faransa kan ta'addanci

Burkina Faso, Mali da Nijar na fama da hare-haren 'yan ta'adda da ke fakewa da yin jihadi.
Ƙasashen Burkina Faso, Mali da Nijar da ke yankin Sahel na Yammacin Afirka na ƙarƙashin mulkin soji / Hoto: AA

Masu gabatar da ƙara a ƙasashen Mali, Burkina Faso da Nijar da ke ƙarƙashin mulkin soji sun ƙaddamar da bincike kan wani ɗan jarida kuma mai bincike ɗan Faransa, Wassim Nasr, suna zarginsa da "goyon bayan ta'addanci" saboda wani bincike da ya gudanar game da ayyukan 'yan ta'adda masu fakewa da sunan jihadi.

Nasr, wanda ke aiki da tashar talabijin ta France 24, ƙwararre ne kan sha'anin tsaro da yake yawan yin sharhi kan 'yan ta'adda da ke da'awar kare Musulunci da suka samo asali daga Mali a 2012, kuma suka yaɗu a yankin Sahel na Yammacin Afirka.

Ya gudanar da zuzzurfan bincike tare da fitar da rahoto game da hare-haren wasu 'yan ta'adda a yankuna masu muhimmanci a Bamako, babban birnin Mali a ranar 17 ga Satumba, kuma kafafan watsa labarai da dama sun rawaito bayanan nasa tare da yaɗa su.

Masu gabatar da ƙara daga sashen shari'a da suka ƙware kan yaƙi da ta'addanci a Mali, Burkina Faso da Nijar sun fitar da sanarwa iri guda, wadda aka sanar a kafafen yaɗa labaran ƙasashen a yammacin ranar Laraba.

Sun zargi Nasr da yin sharhi da "zama mai nuna goyon baya da yaɗa manufofin 'yan ta'adda", suna masu nuni ga harin baya-bayan nan a Bamako da harin 2023 a garin Djibo.

An fara bincike kan Nasr inda ake tuhumarsa da babban laifin haɗa baki wajen ayyukan ta'addanci da goyon bayan 'yan ta'adda, in ji sanarwar.

Nasr yana zaune a Faransa, kuma a wani saƙo da ya fitar ya ce bai yi wani sharhi kan zargin da ake yi masa ba.

"Ina tunanin abokan aiki da ke yankin Sahel, da kuma waɗanda suke fuskantar zubar da jini da kisa daga waɗannan gwamnatoci," ya bayyana a shafin X.

Burkina Faso, Mali da Nijar na fama da hare-haren 'yan ta'adda da ke fakewa da yin jihadi, kuma ƙasashen na ƙarƙashin mulkin soji bayan kifar da gwamnatocin farar-hula tun daga 2020.

Tuni shugabannin ƙasashen suka juya wa ƙawayensu na Yammacin Duniya baya, inda suka ƙulla abota da Rasha, suka kuma fita daga ECOWAS tare da kafa tasu ƙungiyar ta Ƙawancen Sahel.

Hukomomin mulkin soji na ƙasashen sun dakatar da tashar France 24 da wasu kafafen yaɗa labarai na ƙasa da ƙasa daga ɗaukar rahotanni game da ta'addanci a ƙasashen.

AFP