An zabi Gachagua tare da William Ruto a zaben shugaban kasar a ranar 9 ga Agusta na 2022. / Hoto: Reuters

Majalisar Wakilan Kenyan ta kada kuri’ar tsige Mataimakin Shugaban Kasar Kenya Rigathi Gachagua.

‘Yan majalisa 281 ne suka kada kuri’ar goyon bayan tsige shi, yayin da 44 suka kada kuri’ar kin amincewa,sai dan majalisa daya ya kaurace a kur’iar da aka kada ranar Talata.

Akalla kaso biyu cikin uku na ‘yan majalisar – wato 233 – ake bukata su amince da tsige Gachagua kafin matakin ya tabbata.

A yanzu za a kai batun ga Majalisar Dattijai mai mambobi 67, inda idan kashi biyu cikin uku na ‘yan majalisar suka bi sawun takwarorinsu na majalisar wakilai na tsige mataimakin shugaban kasar, to shi ke nan zai bar ofis. Sai dai Gachagua zai iya kalubalantar tsige shi a kotu.

‘Tara kudi ta haramtacciyar hanya’

Daga tuhume-tuhumen da ake yi wa Mataimakin Shugaban Kasar Gachagua akwai zargin tara dukiya ta da kai shillings na Kenya biliyan 5.2, kwatankawacin dalar Amurka miliyan 40.3, a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Wakilin mazabar Kibwezi ta Yamma Mwengi Mutuse, wanda ya gabatar da kudirin tsige Gachagua, ya ce a shekaru biyu da suka gabata, mataimakin shugaban kasar ya karbi albashi na shillings miliyan 24, kwatankwacin $186,000.

Mutuse ya kara da cewa, gabanin zaben shugaban kasa na watan Agustan 2022, Gachagua ya bayyana cewa dukiyarsa ta kai shillings miliyan 800, kwatankwacin $6.8 million.

A cewar Mutuse, akwai “ayar tambaya” kan yadda dukiyar Gachagua ta habaka cikin shekara biyu, yana cewa da alama an tara ta ne ta hanyar rashawa.

Dukiyar ta samu ne daga ‘kasuwanci da dan’uwa marigayi’

An zargi Mataimakin Shugaban Kasar Gachagua, mai shekaru 59 da raina gwamnati, da kuma shiga siyasar kabilanci.

Gachagua, wanda ya bayyana a majalisa ranar Talata, ya musanta zarge-zargen da ake yi masa, inda ya bayyana su a matsayin “tsagwaron karya.”

Mataimakin Shugaban kasar ya ce ya samu dukiyar tasa ne daga kasuwanci daban-daban da suka hada da samar da madarar shanu, da kuma kadarar da ya gada daga marigayin dan’uwansa, Nderitu Gachagua.

A jawabin da ya yi wa ‘yan kasa ranar Litinin, Mataimakin Shugaban Kasar Gachagua ya ce lauyoyinsa za su shigar da kara a kotu, su kalubalanci yadda aka shigar da jama’a cikin batun na tsige shi a makon jiya.

‘Zan yi yaki har sai inda karfina ya kare’

Da yake bayyana shigar jama’a cikin batun na tsige shi, a matsayin wani “dodorido”, Gachagua ya ce matakin da aka bi “ya saba wa kudin tsarin mulki.”

Wasu mutanen kasar sun yi tsammanin Gachagua zai sanar da sauka daga kujerarsa a ranar Litinin, sai dai mataimakin shugaban kasar ya ce a shirye yake ya yi yaki har zuwa “inda karfinsa zai kare” – har da shiga kotu – don tabbatar da cewa bai aikata lafin komai ba.

An zabi Gachagua tare da William Ruto a zaben shugaban kasar a ranar 9 ga Agusta na 2022.

Kafin nan, ya zama dan majalisa daga mazabar Mathira ta Tsakiyar Kenya tun 2017.

TRT Afrika da abokan hulda