Maryam Yusuf wata dalibar jami'a ce kuma ta ce ta yi farin ciki matuka da sabuwar dokar. Hoto: Ahmadu University Zaria

Dalibai a Nijeriya sun bayyana yadda suka ji kan sabuwar dokar da Majalisar Dokokin kasar wadda wa'adinta ke karewa a wannan mako ta yi, wacce za ta rika kare daliban jami'a daga cin zarafi.

Yawanci daliban sun bayyana wa TRT Afrika cewa wannan doka za ta kara musu kwarin gwiwa na tunkarar karatunsu cikin kwanciyar rai, musamman ma dalibai mata.

Majalisar dokokin Nijeriyar ta yi sabuwar dokar ne a ranar Alhamis 8 ga watan Yunin 2023.

Da zarar sabon Shugaban kasar Bola Tinubu ya sanya wa dokar hannu, to ya zama haram ne a dokar kasar malaman manyan makarantu su nemi yin fasikanci da dalibansu.

Kuma duk malamin da aka kama ya kulla alakar masha'a da dalibansa, to zai iya shan dauri har na tsawon shekara 14 a gidan yari.

An fara yunkurin kirkiro sabuwar dokar wadda ke yaki da fasadi a shekarar 2016, sai dai a lokacin dokar ba ta samu karbuwa ba a duka majalisun dokokin kasar biyu ba.

Ko da yake a shekarar 2019, an sake gabatar da dokar a majalisar dattawan kasar bayan wani binciken da kafar yada labarai ta BBC ta yi, wanda ya bankado yadda wasu malamai maza suke cin zarafin dalibansu mata a wasu jami'o'i a Nijeriya da Ghana don su ba su maki a jarabawa.

Binkicen wanda sashin binciken kwakwaf na BBC Africa Eye ya gudanar kuma ya yi masa lakabi da 'Sex for Grades', ya sa mutane sun fusata.

Sai dai an kara samun jinkiri kan zartar da kudurin dokar saboda wasu 'yan majalisar wakilai sun bukaci a yi wasu gyare-gyare - kuma sai kwamitoci biyu na majalisar sun zauna kuma bakinsu ya zo daya kan kalmomin da sabuwar dokar za ta kunsa.

'Yan majalisar suna kokarin kammala ayyukan da suka saka a gaba ne kafin rantsar da sabbin 'yan majalisa a mako mai zuwa.

A farkon watan nan ne wasu dalibai suka fitar da wata sanarwa, inda suka nuna rashin jin dadinsu kan yadda majalisar dokokin kasar ta ki aika wa tsohon Shugaban kasar Muhammadu Buhari dokar don ya sanya hannu kafin ya sauka daga mulki.

Maryam Yusuf wata dalibar jami'a ce kuma ta ce ta yi farin ciki matuka da sabuwar dokar.

"A gaskiya wanan hukunci ya yi saboda wanan zai bai wa dalibai mata karfin gwiwa, don yanzu sun san idan sun kai kara toh za a hukunta mai laifin."

Shi ma wani dalibi a Jami'ar jihar Kaduna Abubakar ya shaida wa TRT cewa ya yi murna da sabuwar dokar.

"Ina goyon bayan wannan doka 100 bisa 100, saboda yadda a kullum matsalar kara yawa take. Idan ana hukuncin daurin shekara 14 ina ganin za a iya magance matsalar," in ji shi.

TRT Afrika