Majalisar Dattijan Nijeriya ta nemi Sufeto Janar na 'yan sanda ya mata bayani kan dubban bindigogin da suka ɓata

Majalisar Dattijan Nijeriya ta nemi Sufeto Janar na 'yan sanda ya mata bayani kan dubban bindigogin da suka ɓata

Majalisar Dattajian Nijeriya ta nuna damuwa matuƙa game da dubban bindigogin da suka ɓace daga ma'aijiyar makamai ta 'yan sandan ƙasar.
Nigeria police

Rundunar 'yan sandan Nijeriya na fuskantar matsin lamba domin ta bayar da bahasi kan wasu makamai da suka ɓace daga wurin ajiyar makamai na 'yan sanda waɗanda suka haɗa da AK-47.

Wani kwamitin Majalisar Dattawan Nijeriya ne ya buƙaci jin bahasin inda ya nuna damuwa game da ɓatar bindigogi 3,907 a ƙasar a shekarar 2020.

Haka kuma kwamitin ya sake duba batun wasu makamai 178,459 waɗanda aka ce sun ɓata daga hannun 'yan sandan, daga ciki har da AK-47 guda 88,078 waɗanda ofishin babban mai binciken kuɗi na Nijeriya ya wallafa batun ɓatan nasa a 2019.

'Makaman da suka ɓace'

“Zuwa watan Disambar 2018, ba a ga jimillar bindigogi 178,459 ba, ciki har da bindigogin AK-47 88,078. Bugu da kari, zuwa watan Janairun 2020, akalla bindigogi 3,907 sun bata,” in ji rahoton.

Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sandan kasa (kan kasafin kuɗi), Abdul Suleiman, ya shaida wa ‘yan majalisar cewa, ‘yan sanda sun yi jawabi a kan tuhumar tare da neman a yi abubuwa a sirrance, yana mai cewa tattaunawa kan batun makaman 'yan sanda ya kamata ya kasance cikin sirri.

“Dubban AK-47 ne suka bace a daidai lokacin da rashin tsaro ya kai kololuwa, ya kamata ‘yan sanda su iya gano wadannan makamai,” in ji wani sanata a kasar.

Rundunar ‘yan sandan ta yi karin haske kan cewa wasu daga cikin makaman da suka bata na jami’an da aka kashe a bakin aiki ne kuma an dauke makamansu. 'Yan sandan sun ƙara da cewa babu makamin da ba a san inda yake ba.

TRT Afrika