Gwamnati ta yi lissafin cewa filin jiragen sama na Jomo Kenyatta na bukatar dala biliyan $2 cikin gaggawa don gyara shi. / Hoto: Reuters

Babbar kungiyar ma'aikatan sufurin jiragen sama ta Kenya ta ɗage yajin aikin da ta shirya yi na makonni biyu wanda aka shirya za a fara daga ranar Litinin din nan.

An ɗage yajin aikin don bayar da damar tattaunawa da gwamnati kan wata yarjejeniya da aka kulla da wani kamfanin India don gyara filin jiragen saman.

Kungiyar da ke wakiltar ma'aikatan filayen jiragen sama, ta nuna adawa da yarjejeniyar da aka sanar a watan da ya gabata cewa da Kamfanin Filin Jiragen Sama na Adani da ke India, wanda ta ce zai janyo rashin ayyukan yi da kawo wadanda ba 'yan kasar Kenya ba su yi aiki a kasar.

"Kungiyar ta yanke hukuncin dage lokacin gudanar da yajin aikin tun da za mu tattauna," in ji sakatare janar na kungiyar Moss Ndiema a ranar Lahadi, yana mai kara wa da cewar za a yi tattaunawar da mahukuntan filin tashin jiragen saman da ma'aikatar sufuri.

"Idan tattaunawar ba ta yi nasara ba wajen cimma matsaya, to kungiyar za ta bayar da sabuwar sanarwa ga mambobinta."

Mahadar sufurin jiragen sama ta yanki

Filin jiragen saman babbar mahadar sufurin jiragen saman yankin ce, kuma yajin aiki na iya janyo babbar matsala ga tafiye-tafiye ta sama a yankin.

Gwamnatin ta kuma ce filin jiragen saman ba na sayarwa ba ne, kuma babu wani mataki mai kama da wannan da aka dauka kan ko za a ci gaba da shirin kulla yarjejeniyar gwamnati da 'yan kasuwa da kamfanin na Adani.

Mahukuntan filin jiragen saman sun ce Adani na shirin gina sabon titin tashi da saukar jirage a Filin Jiragen Sama na Kasa da Kasa na Jomo Kenyatta da kuma inganta ginin idan aka amince da kudirin da suka gabatar.

Gwamnati ta yi lissafin cewa filin jiragen sama na Jomo Kenyatta na bukatar dala biliyan biyu cikin gaggawa don gyara shi, saboda a yanzu filin ba ya iya jigilar fasinjoji miliyan 7.5 a kowacce shekara.

TRT Afrika