Firaministan Libya Abdulhamid Dbeibeh da Hafsan Hafsoshin sojojin ƙasa na Turkiyya Metin Gurak sun tattauna ranar Lahadi game da ayyukan haɗin-kai tsakanin hafsoshin sojojin ƙasa na ƙasashensu tare da gudanar da atisayen soji na haɗin-gwiwa.
A yayin da ya kai ziyarar aiki Libya, Gurak ya miƙa saƙon shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ga Firaminista Dbeibeh inda ya jaddada daɗaɗɗiyar alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu, a cewar wata sanarwa daga gwamnatin Libya.
Ɓangarorin biyu sun tattauna kan haɗin-kai da shirye-shiryen bayar da horo tsakanin ma'aikatun tsaro da hafsoshin sojojinsu tare da gudanar da atisayen soji na haɗin-giwa.
Jakadan Turkiyya a Libya Guven Begec da Hafsan Hafsoshin rundunar tsaron Libya Muhammad Ali Ahmad al-Haddad da mataimakinsa Laftanar Janar Salah Al-Namroush na cikin waɗanda suka halarci taron.
Tun da farko, Gurak ya gana da shugaban Majalisar Fadar shugaban ƙasar Libya, Mohamed al-Menfi, da Hafsan Hafsoshin sojojin Libya Al-Haddad sannan ya ziyarci Ofishin Jakadancin Turkyya a Tripoli.