Hukumar Kwastam ta ce an yi nufin kai kayan jihar Katsina/ Hoto: Hukumar Kwastam

Hukumar Kwastam a Nijeriya mai kula da shiyyar Jihar Kaduna, ta ce a cikin wata guda ta kama buhunhuna dauke da kakin sojoji da kudinsu ya kai naira miliyan 628.

Kwantuloran Kwastam shiyyar jihar Kaduna Musa Jalo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce an kama kayan sojojin ne a tsakanin watan Maris zuwa Afrilun 2023, yayin da ake kokarin shiga da su Nijeriya daga Jamhuriyar Nijar.

“A yayin bincike da jami’anmu suka yi, sun kama wata mota kirar Volkswagen Golf da wani dan kasar Nijar ke tukawa a kan hanyar Jibia zuwa Katsina,’’ a cewar sanarwar.

Buhuhunan kayan soji da hukumar kwastam ta kama daga Nijar/  Hoto: Hukumar Kwastam

Jalo ya kara da cewa, "bayan bincike da muka yi, mun yi wa direban tambayoyi inda muka gano cewa dan kasar Nijar ne kuma yana hanyarsa ta kai kayan ne ga wani da ba a gano ko wane ne ba a Katsina."

A cewar Jalo, tuni aka mika kayayyakin da aka kama zuwa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da masu laifin a gaban kuliya.

Kazalika, sanarwa ta bayyana cewa bisa ga sahihan bayanan sirri, jami’an hukumar sun kama wata mota kirar Mitsubishi Canter dauke da buhunhunan tabar wiwi da aka rufe a cikin buhun garin rogo da dusa, a kan titin Bungudu zuwa Tsafe a jihar Zamfara.

"Bayan an duba motar, an gano tana dauke da buhu 46 na tabar wiwi, da kudinta a kasuwa ya kai naira miliyan 2.1," a cewar sanarwar.

TRT Afrika