Matatar mai ta Dangote ta sanar da karya farashin litar man fetur ɗinta daga ₦950 zuwa ₦890.
Matatar ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar inda ta ce ragin ya fara aiki ne daga 1 ga Fabrairun 2025.
Shugaban sashen watsa labarai na matatar, Anthony Chiejina ya bayyana cewa kasuwa ce ta yi halinta shi ya sa aka samu wannan ragin a halin yanzu.
“Wannan ragin da aka yi an yi shi ne sakamakon sauƙin da aka samu a ɓangaren kasuwannin makamashi da gas na duniya da kuma ragin da aka samu a ‘yan kwanakin nan na farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya,” kamar yadda Chiejina ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar da rare.
Wannan ragin da Dangote ya yi na naira 60 na zuwa ne bayan ya sanar da ƙari a ranar 19 ga Janairun 2025, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a faɗin ƙasar.
Sai dai a halin yanzu, matatar ta Dangote ta bayyana cewa tana fata wannan ragin da ta yi zai je ga jama’a a faɗin ƙasar da kuma jawo raguwar farashin kayayyakin abinci da sauran abubuwa.
A shekarar 2024 ne matatar ta Dangote ta fara aiki gadan-gadan, duk da cewa ta fuskanci jerin ƙalubale kafin da bayan ta fara aiki.
Haka kuma matatar ta Dangote ta rinƙa samun matsala tsakaninta da kamfanin mai na Nijeriya NNPCL kan abubuwa da dama ciki har da batun sayar da mai a cikin ƙasar, sai dai daga baya abubuwa sun lafa a tsakaninsu.