Kwalara ta ɓarke a jihar Borno da ke arewacin Nijeriya, makonni bayan mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye birnin Maiduguri, a cewar Ƙungiyar Likitoci ta jihar.
Ambaliyar ruwan ta lalata tsarin kula da tsaftar muhalli da cibiyoyin samar da ruwan sha.
Shugaban Ƙungiyar Likitocin Elyakub Yakubu Mohammed ya ce an samu mutane 451 da ake zargin sun kamu da cutar, daga cikin dubban mutanen da ambaliya ta raba da muhallansu, inda aka tabbatar da mutane 128 sun kamu bayan an yi musu gwaji.
Ya kara da cewa sai dai an gano mutane 20 da ba su kamu da cutar ba daga cikin waɗanda aka yi wa gwajin.
Shugaban na ƙungiyar likitoci ya yi kira ga hukumomi su ƙarfafa tsarin samar da ruwan sha da tsaftar muhalli, su kuma ƙaddamar da gagarumin shirin riga-kafi, sannan a duƙufa wajen wayar da kan jama'a.
A ranar Juma'ar da ta gabata Kwamishinan Lafiya na jihar ta Borno Baba Mala Gana ya bayyana cewa cutar ta kwalara ta bazu zuwa wasu yankuna huɗu na jihar, bayan mummunar ambaliyar ruwa da aka fuskanta.
Hukumomi a Nigeria sun ce mutane 359 aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon kamuwa da cutar a jihohin ƙasar 36 har da Abuja, babban birnin ƙasar.
Cibiyar Yaƙi da Cututtuka ta Nijeriya NCDC ta kuma ce fiye da mutum 10,000 ne suka kamu da cutar a faɗin ƙasar zuwa ƙarshen makon jiya.
NCDC ta ce matsalar na ƙara ta'azzara tun lokacin da aka fara fuskantar mamakon ruwan sama a damunar bana.
Ta ce rashin tsaftar muhalli da tsaftataccen ruwan sha da kuma yadda mutane suke yin ba-haya a waje, su ne muhimman abubuwan da ke ƙara yaɗa cutar.