Abdirahman Mohamed Abdullahi, da aka fi sani Irro shi ne ya lashe zaɓen na shugaban ƙasa na 13 ga watan Nuwamba inda ya kayar da shugaba mai ci Muse Bihi Abdi. / Hoto: AFP

Kotun Tsarin Mulki ta Somaliland ta tabbatar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na ranar 13 ga Nuwamba, wanda aka bayyana ɗan takarar hamayya Abdirahman Mohamed Abdullahi a matsayin wanda ya lashe.

Gaba ɗaya alkalan kotun sun amince da murya ɗaya cewa an yi zaɓen cikin gaskiya da adalci.

Abdullahi, wanda aka fi sani da Irro, ya lashe zaɓen na shugaban ƙasa ne, inda ya kayar da shugaban mai ci Muse Bihi Abdi.

Irro, wanda ya yi takara a jam'iyyar Waddani ya samu ƙuri'u 407,908, kimanin 64% na ƙur'iun da aka kaɗa.

Fitar masu zaɓe

Bihi, wanda ya yi takara a jam'iyyar Kulmiye, ya samu ƙuri'u 225,519, kimanin 35% na ƙuri'un da aka kaɗa, inda ya zo na biyu.

Wani ɗan takarar kuma wanda ya zo na uku, Faysal Ali Warabe na jam'iyyar UCID, ya samu ƙuri'u 4,699 votes, kimanin 0.7% of na kuri'un da aka kaɗa.

A sakamakon da aka bayyana a hukumance ranar 19 ga Nuwamamba, Shugaban Hukumar Zaɓen Ƙasar ta Somaliland, Muse Yusuf Hassan, ya ce yawan mutanen da suka fita zaɓen na ranar 13 ga Nuwamba ya kai 50%.

Kimanin mutum miliyan 1.2 ne suka yi rijistar zaɓe, amma kusan mutum 648,000 ne suka kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen na baya-bayanna.

Jinkirta zaɓe

Da farko an shirya za a yi zaɓen na Somaliland ne a 2022, amma batutuwa na siyasa sun janyo an jinkirta shi.

Shugaban ƙasar mai barin gado Bihi, wanda tsohon direban jirgin sama na 'yan sanda ne, ya yi shugabancin ƙasar na tsawon shekaru bakwai.

A lokacin yaƙin neman zaɓe, Bihi mai shekaru 76 ya yi alkawarin mutunta sakamakon zaɓen, ko da kuwa ya ya kasance.

Wane ne Irro?

A 2017, Bihi ya kayar da Irro inda ya samu ƙuri'u kusan 306,000 ko kuma %5% na ƙuri'un da aka kaɗa, yayin da Irro ya samu 226,000, kimanin 41% na ƙuri'un.

A saƙonsa na yaƙin neman zaɓe a bana, Irro, mai shekaru 69 ya yi alƙawarin sauye-sauye a fannin tattalin arziki da siyasa, tare da samar da ƙarin ayyukan yi.

An haifi shugaban mai jiran gado Irro a ranar 29 ga watan Afrilu,1955 a Hargeisa.

Ya yi karatun babbar makarantar a babban birnin Somalia, Mogadishu.

Shugaban majalisa tsawon shekara 12

Shafin Intanet na jam'iyyarsa ta Waddani ya ce Irro yana da difloma a harkar gudanarwa daga wata makaranta a Somalia, ya kuma yi digiri na ɗaya da na biyu duka a kan gudanarwa a jami'o'in Amurka

A1981, Ma'aikatar Harkokin Wajen Somalia ta ɗauke shi a matsayin ma'aicin diflomasiyya, inda ya yi aiki a ofishin jakadancin Somalia a Rasha, kafin ya koma Finalnd inda ya zauna da iyalensa a shekarun 1990.

Irro ya koma Somalia a 1999 ya kuma taimaka wajen kafa jam'iyyar Justice and Welfare Party (UCID).

A 2005, an zaɓe shi zuwa majalisar dokokin Somaliland, inda ya shugabanci majalisar tsawon shekara 12.

Maitamakin shugaban ƙasa

A 2012, ya zama cikin mutane biyu da suka kafa jam'iyyar Waddani Party, kuma an zaɓe shi shugabanta na farko, sannan ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2017.

A zaɓukan majalisa da na yankuna a 2021, jam'iyyar Waddani ta samu kujeru mafiya rinjiye.

Kamfanin dillancin labarai na Somalia SONNA ya ba da rahoton cewa Shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamud "ya taya Irro murna, a matsayinsa na sabon shugaban ƙasar Somaliland a arewacin Somalia."

Mohamed Aw-Ali Abdi, shi ne wanda zai kasance mataimakin shugaban ƙasar na Somaliland.

Rantsuwa

Irro da mataimakinsa za su yi rantsuwar kama aiki a watan Disamba.

Somaliland, wacce take iƙirarin samun 'yanci tun 1991, ba a ɗaukanta a matsayin ƙasa a duniya, inda ƙasashen duniya ke yi mata kallon wani yanki ne na Jamhuriyar Somalia.

TRT Afrika