Nasiru Yusuf Gawuna ya rike mukamin mataimakin gwamnan Kano daga 2015 zuwa 2023./Hoto:OTHER

Kotun Daukaka Kara da ke Abuja babban birnin Nijeriya ta tabbatar da Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin halastaccen gwamnan Kano a zaben watan Fabrairun 2023.

Kotun ta kuma bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP ya mika mulki ga Gawuna.

Ta bayyana haka ne a hukuncin da ta yanke ranar Juma'a.

Kotun ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta jihar Kano karkashin jagorancin Mai Shari'a Oluyemi Akintan Osadebay ta yanke wanda ya sauke Abba Kabir Yusuf daga mukamin gwamnan jihar ranar 20 ga watan Satumba.

Labari mai alaka: Kotun zabe ta Kano ta ce Nasiru Gawuna ne yi nasara a zaben gwamnan jihar

A wancan hukuncin, kotun ta cire kuri'a 165,663 daga kuri'un da Abba Gida-Gida ya samu inda ta ce ba su da inganci, tana mai cewa ba a manna wa kuri'un hatimi ba don haka ba sahihai ba ne.

Sai dai jim kadan bayan hakan, Abba Kabir Yusuf ya shigar da kara inda ya kalubalanci hukuncin kotun sauraren kararrakin zaben.

Tun da farko a zaben da aka yi a watan Maris din 2023 Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 1,019,602, sai kuma Nasiru Yusuf Gawuna na APC ya samu 890,705.

TRT Afrika