A jihar Kano da ke arewacin Nijeriya, takaddama ta kaure game da alfanu ko halaccin rushe wasu gine-gine da ke birnin jihar, wadanda gwamnati ta kira haramtattu.
Sabon gwamna jihar Abba Kabir Yusuf, shi ne ke jagorantar wannan aiki a wasu unguwannin cikin birni.
Cikin makon farko na hawansa kan kujerar mulki a jihar da ta fi kowace yawan al’umma a Nijeriya, Gwamna Abba Yusuf ya sanar tare da aiwatar da niyyarsa ta kawar da wasu gine-gine da aka samar "ba bisa ka'ida ba" a lokacin gwamnatin da ta gabata ta Abdullahi Umar Ganduje.
Rahotannin sun nuna cewa gwamnatin jihar ta sanar da kwace kadarori da suka hada da filaye da wuraren da gwamnatin baya ta mallaka wa wasu mutane da kamfanoni, musamman a inda gwamnati mai ci ta ce wuraren amfanin al’umma ne.
Wuraren da ake zargin an handame a baya sun hada da filayen makarantu da asibitoci da kasuwanni da filayen wasa da kotu da makabartu da kuma wuraren tarihi.
Wannan lamari dai ya jawo cece-ku-ce mai zafi ba ma tsakanin 'yan jihar ba kawai, har 'yan sauran jihohi batun na daukar hankulansu.
To ko me masana shari’a da tsarin gwamnati a Nijeriya ke cewa kan dacewar hanyoyin karbe kadarori daga wajen mutane?
TRT Afrika ta tuntubi wasu kwararru kan tsarin mulkin Nijeriya, da kuma siyasar zamantakewa tsakanin gwamnati da al’umma don jin amsar hakan.
Barrister Sani Gwale, masani ne kuma lauya mai zaman kansa, wanda yake gudanar da aikinsa a birnin na Kano, ya sanar da TRT Afrika cewa, “Tsarin mulkin Nijeriya dangane da iko da amfani da kasa, ya dora alhakin kula da kasa da ke kowace jiha kan gwamnan jihar.”
Tsarin mulkin Nijeriya
Barista Sani Gwale ya bayyana cewa, “Bisa sashe na 4 a Jadawali na Biyu na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 (kamar yadda aka yi masa kwaskwarima), ba a ambaci kasa a jerin batutuwansa ba, abin da ya sa hurumi da iko kan kasa suka shiga karkashin alfarmar da gwamononi suke da ita”.
Sannan ya kara da cewa “Dokar Amfani da Kasa ta 1978 ita ta fayyace cewa an mallaka wa gwamna ikon kula da kasa, duk da cewa ta ambaci wasu matakai game da gudanar da wannan iko karkashin dokar tarayyar Nijeriya.
“Amma dai hakkin kula ko rarraba mallaka ko izinin amfani da kasa yana wurin gwamna,” in ji shi.
Lauyan ya kara da cewa, “Sashe na farko na dokar ya damka duka kasar da ke Nijeriya a hannun gwamnoni, a matsayin amana, a maimakon al’ummar Nijeriya.
Gwamna shi ke da ikon mallakawa, da sanya hannu kan takardar mallakar kasa a jiharsa”.
Shi ma Uchechukwu Michael Ogbei, lauya ne mai zaman kansa da yake kamfanin Rosenut Solicitors da ke hedikwata a Legas, a hirarsa da TRT Afrika ya ce “Gwamna shi ke da ikon kasafta kasa, da mallakawa, da sanya haraji ko yafe harajin kasa na shekara-shekara.”
Haka kuma, dokar ta dora wa gwamna alhakin karbe kasa, ko saka haraji kan masu mallakar kasa, da ikon lamuncewa da cinikin kasa, duk da dai dokar ta ce gwamna ya kafa hukuma ko kwamitin kula da bayarwa ko amfani da kasa.
Sai dai kuma a cewar Lauya Sani Gwale, su ma shugabannin kananan hukumomi suna da nasu ikon kan mallakawa ko amfani da kasa da ke kauyuka, duk da cewa suna haka ne da sahalewar gwamnatin jiha.
Dokar amfani da kasa ba tun yau take haifar da takaddama ba. Hasali ma, yawan korafi kan batun ne ya sa ake ta kiraye-kiraye kan shafe dokar amfani da kasa ta 1978, don dabbaka sabuwar doka da za ta dace da zamanin yau, amma abin ya ci tura.
Dalilan karbe kasa bisa dokar amfani da kasa ta 1978
A zantawarsa da TRT Afrika, Lauya Sani Gwale ya bayyana cewa akwai dalilai, sannan akwai hanyoyin da doka ta amince da su wajen karbe mallakar wuri ko gini daga hannun wanda ya mallake su a Nijeriya.
Lauyan ya ce duk da kasar da ke birane su aka bar wa gwamna ya kula da su, yayin da kasar karkara take karkashin kulawar shugabannin kananan hukumomi, to a wajen karbe kasa, gwamna yana da iko kan duka kasar jiharsa ne.
Da farko, ga wasu dalilan da suke sa gwamnati ta karbe wuri ko muhalli.
1) Fifita bukatar al’umma
Wannan ya jibinci fifita bukatar al’umma sama da ta mutum guda, ko mutane kalilan.
Wato duk lokacin da gwamnati ta bukaci amfani da kasa don gina abin more rayuwar jama’a, tana iya karbe wuri ko gina shi, sannan ta mayar da shi na al’umma.
Misali kamar idan tana bukatar wajen don gina makaranta ko kasuwa ko asibiti, ko titi, ko hanyar ruwa, ko duk wani abu da ta ga dacewarsa ko bukatuwarsa wajen al’ummarta.
2) Rashin cika ka’idojin mallaka
Gwamnati tana iya karbe wurare mallakar mutane, a lokacin da ta hakikance cewa mamallakan ba su cika duka ko wani sashe na ka’idojin mallakar kasa da ta gindaya ba.
Misalin hakan akwai rashin gina waje kan lokaci, ko yin gini ba bisa ka’ida ba. Akwai kuma rashin biyan harajin kasa, ko amfani da kasa ko gini wajen aikata haramtattun ayyuka kamar ta’addanci, ko safarar miyagun kwayoyi.
3) Bukata daga gwamnatin tarayya
Duk lokacin da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta nemi wani yanki na kasa da ke fadin Nijeriya, to sai ta tuntubi gwamna ko gwamnonin jihar da yankin ya fada.
Alal misali, idan gwamnati na son yin tituna, ko madatsar ruwa, ko gina asibiti ko makaranta.
4) Samuwar ma’adanai a yanki
Dokar Nijeriya ta nuna cewa duka wani ma’adani da ke karkashin kasar Nijeriya, to mallakin kasa ne, kuma gwamnatin Nijeriya ce ke da alhakin mallaka ko sarrafa wannan albarkatun na kasa.
Wannan ya sa a kowane lokaci da wani ma’adani ya bayyana a wani yanki, ko da mallakin wani ne to gwamnati za ta karbe shi, sannan ta zabi hanyar haka ko amfani da ma’adanin yadda ta so.
5) Rashin neman izinin sayarwa ko mallakawa
Ba duka kasa ce ake bayar da shaidar mallakarta ba. Amma idan wuri yana da satifiket na mallaka ko amfani, to mamallakin yana da ikon sayar da shi, ko kyautar da shi, ko bayar da jinginarsa ga wanda ya so.
Sai dai kuma, akwai sharuddan da doka ta ce a cika yayin wannan ciniki ko sauya mallaka.
Misali akwai sanar da hukumar kula da kasa, da biyan haraji, da tantance sabon mamallakin, da kuma dacewar sabon mamallakin.
Sharuddan karbe fili ko gini daga wajen mutane da tursasawa
Hanyoyin da doka ta tanadar don karbewa ko kwace fili, ko gini, ko wani muhalli daga wajen mutane ala tilas, an tanade su ne don kauce wa zalunci daga bangaren gwamnati, ko masu iya amfani da gwamnati, ko ma’aikatanta. Wasu daga ka’idojin su ne:
1) Bayar da satifiket na karbe kasa
Kamar yadda doka ta ce gwamnati ta bayar da satifiket din mallakar wuri ga wanda ya mallaka, haka nan doka ta ce duk sanda za a kwace wa wani kasa, to sai an bayar da satifiket din kwace kasar ga mamallakinta.
Takardar shaidar kwacewa za ta iya zama abar gabatarwa a kotu ko banki.
2) Bayar da rubutaccen gargadi na karbe kasa
Doka ta ce ba a kwace kasa ba tare da an sanar da mamallakin kasar ba, ko wanda yake wakiltarsa ba.
Wannan sanarwa za ta zo ne a rubuce, kuma sai an danka wa wanda ya mallaka kafin gwamnati ta iya kwace kasar.
Wannan zai bayar da dama ga mutum ya shirya, ko ya kwashe dukiyarsa da ke wurin.
3) Ayyana dalilan kwacewa a rubuce
Wajibi ne gwamnati ta sanar da wanda ya mallaki kasa dalilan da ya sa ta kwace kasar, a rubuce.
Bayar da irin wannan hujja zai taimaka wa wanda ya rasa kadararsa sanin ko ba a zalunce shi ba.
4) Bayar da diyya ga mamallaki
A doka, ba a bayar da diyyar karbe kasa, sai dai diyyar gini ko muhallin da ke doron kasar, sakamakon cewa da ma kasar aro gwamnati ta bai wa mutum.
Amma gwamnati tana iya zabar yin ihisani ga wanda ta karbewa fili.
5) Fayyace adadin diyyar kasa
Doka ta ce kwamitin kwararru wadanda gwamnati ta amince da su ne kadai za a karbi kiyasin su game da kima, ko daraja ko farashin gini ko muhallin da gwamnatin za ta biya diyya kansa.
Me ya sa wasu ke ganin abin da gwamnatin Jihar Kano ke yi ba daidai ba ne?
Wasu da dama dai suna ta sukar gwamnatin Jihar Kanon kan wannan mataki da take dauka na rushe gine-gine cikin kasa da mako guda da hawanta.
Barista Gwale ya ce abin da ya sa ake ganin abin da gwamnatin Kano take ba daidai ba ne shi ne, doka ta ce kamar yadda aka ba da satifiket na bayar da mallakar waje, to haka za a ba da satifiket na kwacewa, bayan an bayar da notis na kwacewar duka a rubuce.
"Wadanda abin ya shafa suna iya gabatar da batutuwa biyu a gaban kotu. Za su roki kotu ta hukunta cewa karbewar ba halastacciya ba ce, sannan su nemi diyyar dukiyar da aka sarayar musu lokacin kwacewar.
A ra’ayin lauya Uchechukwu Ogbei kan wannan batu, ya ce “Babban batun da za a yi takaddama a kai shi ne rashin bayar da notis a rubuce na karbe kasa.
"Notis abu ne mai alaka da lokaci, yayin da satifiket din karbewa gwamnati tana iya kawo shi kuma ta ce ai ta fitar da shi tuntuni.”
“Matukar gwamnati ta karbe kasa ne saboda dalilin sabawa dokar mallaka ko sayarwa, ba wai da nufin fifita amfanin jama’a ba, to ba lallai ta biya diyya ba.”
“Duk kasar da gwamna ya karbe don amfanin al’umma, to haramun ne ya mallakawa wani mutum kuma. Dole a yi amfani da kasar don al’umma,” in ji Mista Ogbei.