Masu laifin suna daga cikin gungun ‘yan a-waren da suka kai hari ofishin ‘yan sanda da ke yankin Mepe da Avevime a ranar 25 ga Satumba na 2020 tare da kwashe motocin ‘yan sanda a Ghana. / Hoto: GNA

Wata babbar kotu a birnin Accra na kasar Ghana za ta yanke wa wasu 'yan a-ware shida hukunci bayan ta same su da laifin yunkurin kafa kasar da ake kira Western Togoland.

Masu laifin sun hada da Gabriel Gorvinoa da Cephas Zodanu da Benjamin Gbadado da Richard Doglo Ametepe da Cosmos Favor da kuma Vincent Ramsayer Atsu Gale, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ghana News Agency ya rawaito.

Mai shari'a Mary Maame Ekue Yanzuh da ke sauraron karar, ta kuma dage zaman kotun zuwa ranar Laraba 1 ga watan Nuwanba domin yanke hukunci.

Masu laifin suna daga cikin gungun ‘yan a-waren da suka kai hari ofishin ‘yan sanda da ke yankin Mepe da Avevime a ranar 25 ga Satumba na 2020 tare da kwashe motocin ‘yan sanda a Ghana.

Kazalika sun yi awon-gaba da makamai da kuma sace jami’an da ke bakin aiki.

'Yan sanda sun sake rike mutane biyu da aka ba da belinsu yayin da ake tuhumarsu har sai ranar 1 ga watan Nuwamba da kotu za ta sake zama.

Bayan mutane biyun da aka soke belinsu, kotu ta kuma sallami hudu daga cikin mutane 10 wadanda tun farko ake tuhumarsu da irin wannan laifi.

A ranar 25 ga Satumban shekarar 2020 'yan a-waren Western Togoland suka ayyana samun 'yancin kai daga Jamhuriyar Ghana.

Western Togo dai kasa ce da ba a amince da ita ba a hukumance, sannan kasashen duniya na daukarta a matsayin wani bangare na kasar Ghana.

TRT Afrika