A bara Kenya ta fara dasa bishiyoyi domin tsayar da gurbacewar muhalli/AA

A wata rana mai matsakaicin yanayi a cikin watan Yulin shekarar 2019, kasar Habasha ta dasa bishiya miliyan 350 a wani yunkurin nuna jajircewa da kuma juriya da ba a taba ganin irinsa ba.

Kafin wannan dashen na miliyoyin bishiyoyi babu komai sai labarin rashi da radadi.

A kiyasin Majalisar Dinkin Duniya, yawan bishiyoyin da ke dazukan kasar Habasha sun ragu da kashi 4 cikin 100 daga kashi 35 a karnin da ya gabata.

Wadannan alkaluman da kuma alamun zahiri na matsalar sauyin yanayi da ke dada karuwa – kamar fari da rashin samun isasshen amfanin gona da kuma tsananin zafi ne suka sa kasar ta tsunduma cikin fafutuka.

Kasashen Afrika masu yawa ne suka bi sahun Habasha wajen kwaikwayon dasa bishiyoyi masu yawa domin magance tasirin sauyin yanayi da karuwar yawan jama’a da kuma yin amfani da fili ta hanyar da ba za ta dore ba.

Lamarin zai zama dogon yaki ga nahiya ta biyu mafi yawan jama’a a duniya.

Ceton bishiyoyi

Fari na yi wa kasashen Gabashin Afirka da dama illa/AA

Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce Afrika ta Gabas da kuma yankin kusurwar Afrika, na fama da matsanancin fari na tsawon lokaci inda ake tsammanin shekara ta biyar a jere da ba a samu ruwan sama da damina ba zai sa a sake tsunduma cikin mummunan yanayin rashin abinci.

A wasu sassan Kenya da Somaliya da Habasha, lokacin rani ya fi tsawo da kuma tsanani cikin ‘yan shekarun nan, kuma yana shafar mutum sama da miliyan 36, in ji MDD.

A watan Nuwamban bara, kungiyoyin ayyukan jin kai sun yi gargadin cewa karancin ruwan sama ka iya cigaba a damunar bana daga watan Maris zuwa Mayu na shekarar 2023. Sun bayyana rashin ruwan saman a matsayin “bala’in da ya shafi bil adama”.

A nazarin da ta yi a watan Janairun shekarar 2023, hukumar kula da fari ta Kenya ta bayyana cewa ruwan da aka yi a tsakanin watan Oktoba zuwa Disamban shekarar da ta gabata ya yi karanci sosai.

Bayan damuna hudu da ba a yi isasshen ruwa ba, farin ya yi tsanani a wasu sassan kasar, in ji hukumar.

Hukumar ta yi kiyasin cewa sama da mutum miliyan 4.4 ka iya bukatar taimako a shekarar 2023.

"Yawan bishiyoyin da ke dazukan kasar Habasha sun ragu da kashi 4 cikin 100 daga kashi 35 a karnin da ya gabata."

MDD

A daidai lokacin da tasirin sauyin yanayi ya fara bayyana, a bara Kenya ta fara dasa bishiyoyi domin tsayar da gurbacewar muhalli.

A watan Disamba, Shugaba William Ruto ya kaddamar da gangamin dasa bishiyoyi da kuma gyara muhalli inda ake son dasa bishiya biliyan 15 zuwa shekarar 2032.

“Idan kowa daga cikinmu zai ba da tasa gudumawar, to hakan na nufin duk dan Kenya daya zai dasa bishiya 300 a cikin shekara 10 wato duk shekara mutum daya zai dasa bishiya 30,” in ji sakataren ma’aikatar kula da muhalli da gandun daji a wajen kaddamar da gangamin.

Kasar Habasha ta cigaba a kan turbar da ta zaba a shekarar 2019.

Mutane na aikin dashen bishiyoyi a kasar Habasha/AA

Ofishin kula da shirin kare muhalli na Majalisar Dinkin Duniya (UNEP), ya ce mayar da martabar yanayin muhalli ka iya cigaba da inganta rayuwa na tsawon lokaci.

Levis Kavagi, wanda yake lura da shirin kare muhalli da kuma bambancin halittu na ofishin UNEP na Afrika, ya bayyana wa TRT Afrika cewa samar da gandun daji da kuma sabunta gandun daji wasu hanyoyi ne na sake tattara iskar da muke shaka ta carbon dioxide da kuma adana ta a cikin dazuka.

“Tasirin samar da ko kuma sabunta gandun daji zai dogara ne kan yadda tsire-tsire suka rufe kasa. Iya yawan yadda suka rufe kasa, iya tasirin.

"Kebetattun bishiyoyi na da kayyadadden tasirin da ake bukata wajen samar da daidaito a yanayin wani yanki.

“Idan suka kai yadda ya kamata, gandun daji na ba da gudunmowa wajen daidaiton yanayi da kuma yanayin ruwa na yankin,” in ji Kavagi.

Fari na jefa 'yan Afrika da dama cikin bala'i\AA

Ya kara da cewa bishiyoyi sun fi bunkasa a wuraren da irinsu suke a da.

“Saboda haka, ya fi kyau a dasa bishiyoyi a irin muhallin da suke a da inda yiwuwar samun iri mai barazana zai ragu.

“Na biyu, ire-iren da ake samu a wuri sun saba da yanayi da kuma kasar wannan wurin kuma sun fi yiwuwar daukar mabambantan halittu fiye da ire-iren da aka dauko daga waje.

"Da zarar sun kama kasa ire-iren da suka saba da wuri za su hayayyafa ba tare da taimako ba.”

Muhammed Lamin SaidyKhan na kungiyar Climate Action Network (CAN), ya ce shuka bishiyoyi a wuraren da ke fama da fari dole su kasance a hankali a hankali. Climate Action Network wata gamayya ce ta kungiyoyin fararen hula da ke yaki da matsalar sauyin yanayi.

“Akwai bishiyoyin da ke bas a mutuwa murus ko da a yanayi na fari ne, wadanda za a iya farfado da si. Sannan idan aka sa muhallin ya sake zama kore, zai ba da damar shuka kowace irin bishiya.”

Lamin ya jaddada cewar idan ana son shirin dasa bishiyoyi na kasashe ya rinka dorewa, dole gwamnatoci su rinka ware kasafin kudi kan hakan, da kuma bayar da kwarin gwiwar tuntubar mutanen gari kai tsaye.

Har mata ma ba a bar su a baya ba wajen aikin dashen bishiyoyi don ceton muhalli/AA

Sai dai kuma UNEP, ta yi gargadin cewa an tafka kura-kurai wajen sabunta gandun daji da kuma dasa bishiyoyi.

“Alal misali, idan aka yi amfani da irin da bai dace ba da hanyar da ba ta dace ba a wuraren da ba su kamata ba, ba tare da hadin gwiwa tsakanin masu aikin da masana kimiyya da kuma mutanen gari ba, to fa mutane yanayi za su samu matsalar mamaya daga wasu halittun kamar kwari daban-daban a lokuta da dama,” in ji Kavagi daga UNEP.

“Dukan yanayin muhalli daga jigawa zuwa fadama, daga kololuwar dutse zuwa kasan teku – suna da muhimman gudunmowa da suke bayarwa kuma suna adana halittu mabambanta. Dasa bishiyoyi a jigawa ka iya bata muhalli fiye da gyara shi.”

TRT Afrika