Akasarin jama'ar Kenya sun fi son siyan takalma gwanjo saboda sauƙinsu da inganci. / Hoto: Reuters

Gwamnatin Kenya za ta dakatar da shigar da takalma cikin ƙasar nan ba da jimawa ba, kamar yadda shugaban ƙasar William Ruto ya bayyana.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin kasar ta shafe kimanin guda tana ƙoƙarin kafa masana’antun jima a ƙasar da ke Gabashin Afirka.

“Yana da muhimmanci ga dabarunmu mu sauya darajar yadda ake fitar da fata a yadda take tsurarta zuwa wadda aka gyarata da kyau ga kamfanoni,” kamar yadda Ruto ya bayyana a wani jawabi da ya yi a ranar Asabar a yayin bikin Madaraka – bikin tunawa da ranar da Kenya ta soma samu ‘yancin kanta daga Birtaniya.

Ya ce gwamnati na bunkasa sana’o’in cikin gida don sarrafa fatu domin samun kayayyaki masu inganci.

Na yi wannan alkawari, cewa nan ba da jimawa ba, za mu daina shigo da takalma daga ko'ina.

Za mu rinƙa saka takalmanmu; da aka yi a Kenya, muna amfani da fatunmu,” kamar yadda kafofin watsa labarai na ƙasar suka ruwaito Mista Ruto na cewa.

Gwanjon takalma

‘Yan Kenya da dama sun fi son sayen gwanjon takalma waɗanda aka yi amfani da su a ƙasashen waje, sakamakon sun fi ƙwari da kuma sauki.

Ana alaƙanta kayayyakin da aka samar da su da fatu a cikin gida da yanayi na wadata.

A jawabin da ya yi, Mista Ruto ya ce an ware kimanin shilling miliyan 40, kimanin dala miliyan uku kenan domin bunƙasa wani kamfanin ƙasar na jima.

Za a yi amfani da kuɗin domin sayen injina na zamani da gina wurin yin haɗa takalma da kuma tattara fatu.

TRT Afrika