Daga Halima Umar Saleh
Ana samun karuwar faruwar Guguwar Hamada mai tsanani a wasu sassan nahiyar Afirka, wacce dama take fama da bala'o;in sauyin yanayi daban-daban da suka hada da fari da tsananin zafi da ambaliyar ruwa da mahaukaciyar guguwa da kuma karuwar ruwan teku.
Wannan bala'i na Guguwar Hamada na jawo asarar dukiyoyi da raba mutane da muhallansu da sauran abubuwa.
Guguwar Hamada da aka yi a baya-bayan nan ita ce wacce ta shafi kasar Kamaru a watan Fabrairun 2023, inda rairayi da yashin da suka taso daga Hamadara Saharar Afirka suka turnuke kusan rabin kasar, musamman ma yankin arewaci.
Ministan sufuri na Kamaru Ernest Ngalle Bibehe, ya ce "kusan rabin kasar" ya fuskanci barazanar guguwar hamada wacce ta tsayar da harkokin sufuri tare da jawo matsalolin cutukan numfashi a yankunan da abin ya shafa.
Ramat Hassan wani masunci mai shekara 23 mazaunin garin Darak ne a gundumar Maroua da ke yankin Arewa mai nisa na Kamaru, ya tuna yadda shi da abokan sana’arsa suka firgita sosai har suka gaza ci gaba da kamun kifin da suke yi a yayin da guguwar ta tunkari yankinsu.
Ya ce: “a lokacin da kurar ta zo da iska mai karfi, sai ko ina ya lullube ya yi duhu dundum. Ba ma iya ganin ko da kogin da ke gabanmu da muke kamun kifi a wajen,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Malam Hassan ya kara da cewa da kyar suka laluba suka gano hanyar gida “amma akwai abokan sana’arsa da dama da suka bata, sai washe gari suka iya komawa gida.”
Malam Hassan ya ce guguwar ta jawo wa “mutane da yawa mura mai tsanani da tari, ni ma sai da na kamu.”
A bara ma, an yi irin wannan guguwa a wasu yankuna na arewacin Nijeriya, lamarin da ya jawo tsaiko ga harkokin tattalin arziki da na yau da kullum.
Duk da cewa babu alkaluma a hukumance na wadanda abin ya shafa da barnar da ta yi, wasu mazauna jihar Borno a arewacin Nijeriya sun shaida wa TRT Afrika cewa lamarin ya munana kuma ya sa ciwukan masu fama da asma da ciwukan numfashi sun tashi, tare da janyo wa yara da tsofaffi mummunar mura da tari.
A watan Yunin 2018 ma, an yi wata mummunar guguwar hamada a yankin Kudu da Hamadar Sahara na Afirka a kasashe irin su Chadi da Nijar da Arewacin Nijeriya da Mali da da Benin da Ghana da Ivory Coast da kuma Burkina Faso.
Jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Nijeriya na daya daga cikin wuraren da abin ya shafa sosai.
Wani mazaunin garin Malam Aminu Makama, ya gaya wa TRT Afrika “mutane da yawa sun tsorata har wasu sun zaci kamar tashin duniya ne."
Malam Aminu ya ce yana tunawa abin ya faru ne kwana daya bayan karamar sallah. “Gidaje da gine-gine da dama sun lalace, mutane sun firgice, manyan bishiyoyi sun yi ta faduwa tun daga tushensu, sannan kuma an samu hadurra na ababen hawa,” in ji shi.
“A lokacin dai hukumomi sun ce mutum biyu ne kawai suka mutu, amma maganar gaskiya mutanen da muka san sun rasa rayukansu sakamakon guguwar nan suna da yawa. Wasu ma gini ne ya fada musu suka mutu a karkashin baraguzai,” Malam Aminu ya kara da cewa.
Kasashen Arewacin Afirka da na Gabas ta Tsakiya ma suna fuskantar irin wannan bala’i lokaci zuwa lokaci.
Alal misali, a watan Mayun shekarar 2022 sau takwas ana guguwar hamada a kasar Iraki daga tsakanin watan Afrilu zuwa Mayu, inda aka kwantar da daruruwan mutane a asibiti tare da dakatar da tashi da saukar jiragen sama.
Ta yaya guguwar hamada ke tashi?
Masana kimiyya sun ce guguwar hamada na faruwa ne a yayin da iska mai karfi ta kwashi rairayi mai yawa daga sahara ta yi tafiyar dumbin kilomitoci da shi. Guguwar hamada na faruwa ne a yankunan da suke da zafi wadanda kuma suke a bushe.
Wani kwararre a kan harkar muhalli a Kamaru, Dr. Bindowo Aboubakari ya ce guguwar hamada yawanci kan faru ne “yayin da nau’ukan iska masu karfi suka ci karo da juna.”
Hakan na nufin da zarar an samu wannan cin karo, to sai guguwa mai karfi mai cike da kura ta shafi yankunan da ta tunkara,” in ji shi.
A cewar Mohammed Jafaru Dankwabia, Mataimakin Darakta a Cibiyar Bincike kan Sauyin Yanayi da Samar da Abinci ta Ghana, “kakkarfar guguwa mai dauke da kura da ke gudun kusa kilomita 70 zuwa 100 a cikin sa’a guda abin damuwa ne sosai.
“Ganin yadda guguwar hamadar nan ke shafar yankunan Afirka da dama daga arewa zuwa tsakiya da yamma da ma sauran wuraren nahiyar, lallai abin damuwa ne sosai,” in ji Mr Dankwabia.
Babban Bankin Duniya ya ce asarar da guguwar hamada ta janyo a fadin duniya ya kai ta dala tiriliyan 3.6.
Mene ne ke jawo guguwar hamada a Afirka?
Guguwar hamada na faruwa a Afirka a lokacin da nahiyar ke fama da matsalolin sauyin yanayi daban-daban da suka hada da tsananin zafi da bala’in ambaliya da tumbatsar ruwan teku, wadanda duk suke jawo asarar rayuka da dumbin dukiya da kuma raba mutane da muhallansu.
Kwararru suna dora alhakin wannan mummunan yanayi a kan tasirin sauyin yanayi. Dr. Bindowo Aboubakari ya cewa TRT Afrika “dumamar da duniya ke yi na daga cikin abubuwan da suka sa ake samun guguwar hamda mai tsanani a Afirka, lamarin da ke uzzura sauran al’amuran zamantakewa na nahiyar.
Ya ce “guguwar hamada na daga cikin munanan bala’o’in sauyin yanayi da ke faruwa a duniya.”
Shi ma masani Mr Dankwabia na Ghana, ya ce tasirin sauyin yanayi a kan rayuwarmu “na da matukar yawa.”
Mr Dankwaiba ya shaida wa TRT Afrika cewa ‘’daya daga cikin tasirin sauyin yanayi shi ne guguwar hamadar da ake samu akai-akai a yankin Kudu da Hamadar Saharar Afirka dama sauran yankunan nahiyar a yanzu.”
Kwararru sun ce kusanci yankunan da kasashen da hamadar Sahara na kara saka su cikin barazanar fuskantar guguwar.
Sun ce ayyukan dan adam ma kamar su sare dazuka da diban kasa da kona dazuka na sa waje ya bushe karkaf ba tare da makari ba.
Mr Dankwaiba ya ce “da yawanmu muna ganin cewa sauyin yanayi abu ne daga Allah. Amma kuma a yanzu ayyukan dan adam na sawa yana kara tsanani, kuma ba ma mayar da hankali sosai kan tasirin hakan.”
Wadanne matakan kariya ya kamata a dauka?
A ta bakin wata hukuma ta kasashen Arewacin Afirka da Gabas ta Tsakiya mai wayar da kai kan illar sauyin yanayi, EcoMENA, ta ce za iya rage tasirin guguwar hamada ta hanyar daukar matakan kariya da dama na fannin lafiya da kuma na muhalli.
Ta ce daya daga cikin irin wadannan matakan su ne kara yawan bishiyoyi da tsirrai a Afirka. Hakan zai taimaka wa kasa da yashi da rairayin wajen daina habaka su kuma zama kariya ga yanayi, in ji EcoMENA.
Sannan kwararru sun yi amanna cewar dasa tsirrai da bishiyoyin da aka san su sosai a yanki za su iya rage karfin iskar da tashin guguwar tare da sanya wa rairayin ya yi laushi.
Kasashen Afirka kamar su Habasha tuni suka kaddamar da irin wannan tsari, inda a watan Yulin shekarar 2019 gwamnati ta ce ta dasa irin bishiya har miliyan 350 a rana daya, a matsayin daya daga cikin irin nata yunkurin na ceto muhalli.
Kasashen Afirka da dama sun bi sahun Habasha na bin tsarin shuka bishiyoyi don dakile tasirin sauyin yanayi.
Haka kuma, Mr Dankwaiba ya shawarci kasashen Afirka da su kara azama “wajen shuka bishiyoyi sosai tare da tsare su. Ba wai a shuka su ba kawai, ya kamata a tabbatar an kula da su bayan shukawar.”
“Hakan zai taimaka wajen ba da kariya a lokacin da rana ta gusa daga yankin Sahel, kuma idan babu irin wannan kariyar, to ba za mu iya rage karfin guguwar hamadar nan ba,” ya kara da cewa.
A tsara gine-gine a tsara manufofi
EcoMENA ta bayyana cewa yana da matukar muhimmanci a dinga tsara gine-gine yadda ya kamata a kuma yi gwajin yadda ginin zai iya jurar kadawar iska, musamman a yankunan da suka fi fuskantar irin wannan yanayi.
Baya ga yin shiri na musamman na tsare-tsare gabanin faruwar masifar, Bankin Duniya ya ce ya kamata gwamnatoci a fadin duniya su tsara manufofi na rage tasiri da radadin guguwar hamada, a matakin kasa da kuma duniya baki daya.
Hukumar Hasashen Yanayi ta Duniya a taronta karo na biyar a 2007, ta kaddamar da wani tsari na hasashen guguwar hamada, da nufin karfafa kasashe don su dinga daukar mataki da wuri, a sa ido da yada bayanai ga sauran sassa gabanin faruwar guguwar hamadar.
Ilimi da sauyin yanayi
Kwararre kan sauyin yanayi Mr Dankwaiba ya yi amannar cewa ilimi shi ne ginshiki na sanar da mutane game da illar sauyin yanayi, “kuma hanyar bin wannan mataki ba a baki kawai ya kamata ya tsaya ba, dole ne a yi shi a aikace.”
Duk da cewa Afirka na daga cikin yankunan da wannan lamari ya fi shafa, har yanzu mutanen nahiyar ba su da isasshen ilimi a kan hakan.
“Don haka ilimi na daya daga cikin abubuwan da dole ne mu mayar da hankali a kai don sanar da mutane ainihin abin da ke faruwa da mu da kuma irin barazanar da sauyin yanayi yake yi mana,” a cewar Mista Dankwaiba.
Ya kara da cewa “idan mutane suka fahimci wannan, to sai kuma mu fara tsara yadda za mu farfado da dazuzzukanmu, da magance zaizayewar kasa da kuma sare bishiyoyi, wadanda a ko yaushe su ne manyan abubuwan da ke jawo guguwar hamada.
Ya yi kira ga kasashen duniya da su hada hannu wajen magance illar sauyin yanayi da sauran bala’o’in da ke shafar muhalli a Afirka “saboda idan ba a magance wadannan matsaloli na sauyin yanayi ba, tabbas hakan zai shafi batun samar da abinci a duniya.”
Mutane su dauki matakin kare lafiyarsu
Kwararru sun ce baya ga daukar matakin kare muhalli, ya kamata mutane su dauki matakin kare kansu da lafiyarsu kuma a yayin da duk guguwar hamada ta faru.
Dr. Bindowo Aboubakari ya ce daukar matakai masu sauki kamar sanya takunkumi wanda aka tsara don hana kananan abubuwa shigewa baki da hanci da ido, na da muhimmanci.
“Yana da kyau mutum ya nemi mafaka a lokacin da guguwar hamadar ta taso. Za a iya hawa sama kan tsauni tun rairayin guguwar shi neman sauka kasa yake yi.”
Ya kara da cewa hakan na da muhimmanci matuka wajen rage yiwuwar tarkacen da iskar ta kwaso su same ka.