Fiye da mutane miliyan 600 a faɗin duniya suna fama da matsanancin ciwon baya. Photo / Reuters Fiye da mutane miliyan 600 a faɗin duniya suna fama da matsanancin ciwon baya. Photo / Reuters

Daga

Sylvia Chebet

Hukumar WHO ta bayyana ƙa'idoji game da kula da ciwon baya (LBP) waɗanda suka zayyana wa ma'aikatan lafiya matakan da ya kamata su ɗauka - waɗanda za a yi amfani da su da kuma waɗanda ba za a yi amfani da su ba lokacin aikin kula da lafiya.

Ƙa'idojin sun hana amfani da magungunan kashe raɗaɗin ciwo wanda zai iya sa wa a dogara da su ko kuma a dinga shan su fiye da kima. Kuma sun hana wasu magunguna da ke buƙatar taɓa jiki kamar janye janyen gaɓɓai - da amfani da igiya.

Waɗannan na daga cikin aikin kula da lafiya guda 14 da WHO ta ce za su iya cutarwa fiye da amfanarwa kuma kar a yi amfani da su a-kai-a-kai.

A maimakon haka, an shawarci ƙwararrun ma'aikatan lafiya su taimaka wa marasa lafiya su ilmantar da kansu game zaɓi da kuma dabarun kula da kai da ake da su sannan su tallafi tunaninsu.

Haka kuma, WHO ta fi ganin tasirin yin amfani da maganin da ba sai an yi tiyata ba kamar motsa jiki, da kuma janye janyen gaɓɓai kamar ƴan dabarun da ake yi wa laka da yin tausa.

Mataki na bai-ɗaya

"Magance matsanancin ciwon baya yana buƙatar mataki na bai-ɗaya da kuma biyan buƙatun mara lafiya. Hakan na nufin yin la'akari da yanayin mutumin na musamman da kuma abubuwan da ka iya haddasa ciwon da yake ji," a cewar Dr Anshu Banerjee Darakta a WHO mai kula da Lafiyar Uwa, da Sabbin Haihuwa da Ƙananan Yara da Masu Ƙuruciya da kuma Tsofaffi.

"Muna amfani da waɗannan ƙa'idojin a matsayin abubuwan da za mu tallafa wa mataki na bai-ɗaya wajen kula da matsanancin ciwon baya, domin kyautata ingancin, da kiyayewa da kuma samar da kulawa."

Sababbin ƙa'idojin na WHO sun ɗan makara amma an ce da babu gwamna babu daɗi," Dr Hamisu Kote Ali, wani likitan gaɓɓai da fisiyo ya gaya wa TRT Afrika.

"Likitan zamani ya yi watsi da shika shikan aikin likitanci; da farko ka zamo malami ga mara lafiya sannan na biyu, gudanar da binciken ƙwaƙwaf na zahiri da ya zarce wanda aka saba yau da kullum," Dr Hamisu ya koka.

Ya jaddada cewa yana da muhimmanci a binciki tarihin mara lafiya ciki da waje, tun daga yarintarsu, domin gano abin da ya haddasa ciwon. Hakan zai jagoranci ma'aikatan lafiya wajen samar wa marasa lafiyarsu hanyar tafiyar da ciwon da ta dace.

Ƙa'idojin na WHO sun jaddada cewa yakamata a tsara kulawa ta yadda za ta magance gamayyar matakai (na zahiri da na tunani da na zamantakewa) da za su iya yin tasiri kan matsanancin ciwon bayan mara lafiya.

"Wataƙila a buƙaci tarin kulawa domin magance matsanancin ciwon bayan mutum, a maimakon kulawa guda ɗaya tal da ake amfani da ita a keɓe," WHO ta ce.

Ciwon da ya fi haddasa nakasa

Ciwon baya cuta ce ta gama gari da galibin mutane ke fama da ita a wani lokaci a rayuwarsu kuma ta gaba gaba wajen haddasa nakasa a faɗin duniya.

Alƙaluma daga WHO sun nuna cewa a shekarar 2020, ƙiyasin ɗaya daga cikin mutane 13, wanda ya yi daidai da mutane miliyan 619 sun yi fama da ciwon baya. Wannan ƙarin kashi 60 ne daga 1990.

WHO ta shawarci ma'aikatan lafiya da su tallafa wa buƙutun zahiri da na tunanin marasa lafiya Photo Reuters

Ciwon baya yana shafar ingancin rayuwa kuma yana tattare da da rashin lafiya da kuma hatsarin a rasa rai. Ciwo mai naci na rage wa mutum azamar gudanar da sha'anin iyali da na zamantakewa da kuma aikace-aikace.

Hakan zai iya mummunan tasirin kan lafiyar ƙwaƙwalwarsu sannan ya jawo babbar ɗawainiya wa iyali da al'umma da kuma tsarin kiwon lafiya.

Masu fama da matsanancin ciwon baya, musamman tsofaffi, za su fi saurin faɗawa cikin talauci, da barin aiki kuma wataƙila ba su da wadataccen kuɗin da suka tanada domin gudanar da rayuwa idan sun yi ritaya.

WHO ta lura cewa magance matsanancin ciwon baya tsakanin tsofaffi zai iya saka wa mutum ya tsufa da ƙarfinsa, domin waɗanda suka manyanta su samu kuzarin kulawa da kansu.

Ciwon da ba za a kawar da kai a kansa ba

Matsanancin ciwon baya na nufin ciwo ne da yake shafe sama da watanni 3 bai tafi ba, kuma ba wata cuta ko wasu cututtuka ne suka haifar da shi ba.

WHO ta ce tana sane da bayanan aƙalla kaso 90% na ciwon baya a matakin farko, saboda haka, ta fitar da ƙa'idoji domin jinyarsa.

Sababbin ƙai'dojin sun buƙaci ƙasashe su ƙarfafa kuma su inganta tsarin kiwon lafiyarsu da ayyukan jinya da za su samar da kulawar da aka bayar da shawara a bayar.

"Idan ana so a cim ma ƙudurin samar da kiwo lafiya a ko'ina a duniya, ba za a watsi da batun ciwon baya ba, domin shi ne kan gaba wajen haddasa nakasa a faɗin duniya," Bruce Aylward, Mataimakin Babban Darakta Mai Kula Da Shirin Samar Da kiwon Lafiya A Ko'ina na WHO ya ce.

“Ƙasashe za su iya magance wannan da ake samu a ko'ina, amma a yawancin lokaci su kau da kai kan ƙalubale ta hanyar yin amfani da muhimman matakan bayar da kulawa, yayin da suke ƙarfafa matakansu a kiwon lafiya a mataki na farko," Dr Aylward, wanda shi ma likita ne, ya daɗa a kai.

Daina bayar da kulawa da ba su da tasiri shi ma yana da muhimmanci daidai da ƙa'idojin.

"Idan muka yi haka, za mu iya yin aiki da wasa idan muna shekarun tsufarmu saboda za mu kasance tare da kuzarinmu da tunaninmu cikakku," Dr Hamisu ya gaya wa TRT Afrika.

TRT Afrika