Kamfanin Moderna da gwamnatin Kenya sun kulla yarjejeniya a 2022 inda a wannan makon ne aka kammala cimma matsaya kan aikin / Photo: AFP

Kamfanin hada magunguna na kasar Amurka wato Moderna ya bayyana cewa zai bude reshe a kasar Kenya domin samar da rigakafi.

Ana sa ran kamfanin zai rinka samar da akalla rigakafi miliyan 500 a duk shekara, kamar yadda wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Alhamis ta bayyana.

Moderna ya bayyana cewa cimma matsaya da aka yi da gwamnatin Kenya kan batun rigakafin “wani ginshiki ne na shirinmu na kiwon lafiya a duniya”.

Kamfanin na Moderna zai taka muhimmiyar rawa a Afrika a bangarorin da “ake da bukatu ta bangaren kiwon lafiya da suka hada da cututtuka na numfashi da kuma cututtuka kamar su HIV da sauran masu yaduwa da ke barazana kamar Zika da Ebola,” in ji Stephane Bancel, Shugan kamfanin na Moderna.

Kamfanin samar da magungunan ya kuma bayyana cewa yana sa ran sabon reshen nasa zai rinka samar da magunguna ga Kenya da kuma nahiyar Afirka baki daya da kuma biyan bukatu na gaggawa da ake da su ta fannin lafiya a nahiyar.

Shugaban Kenya William Ruto ya bayyana jin dadinsa kan wannan ci gaba inda ya ce “wannan aikin ba wai Kenya kadai ba zai taimaki nahiyar Afirka ne,” in ji shi.

Babu tabbaci kan yaushe za a soma aikin ginin, amma wannan ne zai zama reshen kamfanin Moderna na farko a Afrika.

Kamfanin Moderna dai na daga cikin kamfanonin rigakafi da suka kirkiro rigakafin korona. An kuma yi amfani da rigakafin kamfanin a kasashe da dama na duniya.

TRT Afrika da abokan hulda